KANUN LABARAI
PDP ta bukaci ‘yan sanda su kama Abdullahi Abbas
Aminu Abdullahi
Jam’iyyar PDP ta bukaci babban sifeton yan sanda na kasa Muhammad Adamu da kama tare da gurfanar da shugaban jam’iyar APC na jihar Kano Abdullahi Abbas bisa kalaman tunzura jama’a da yake yi.
Kano Focus ta ruwaito cewa shugaban jam’iyar PDP na jihar Kano Wada Sagagi ne ya yayi kiran ta cikin wata sanawa da jam’iyyar PDP ta fitar ranar Litinin a nan Kano.
Ta cikin sanarwar Wada Sagagi ya ce tuni suka aike da takarda zuwa ga babban sifeton ‘yan sandan da sauran hukumomin gwamnati domin daukar matakin da ya kamata.
Ya ce ko kadan basu yi mamaki ba don kuwa dabi’ar Abdullahi Abbas ce yin kalaman tunzuri ga magoya bayan su.
“Gare mu wannan ba wata barazana ba ce da za ta hana al’ummar jihar Kano zabar abinda suke so ba.
“Sai dai duba da yadda Demokradiya take, irin wadannan kalaman ana bukatar a dauki mataki a kansu,” a cewar sa.
Idan za a iya tunawa dai a baya bayan nan ne Abdullahi Abbas ya yi wasu kalamai da jam’iyar adawa ke kallon su a matsayin kalaman tunzuri.
Cikin kalaman da suke zarginsa da yi akwai jawabin da ya yi lokacin rantsar da shugabanin kananan hukumomi 44.
“Ku farmaki tare da hukunta duk wanda ya yi yunkurin satar akwati yayin zaben 2023.
“Ku dauki mataki a hannunku kuma ba abinda zai faru.
“Na baku umarni ku hukunta duk wanda ya yi kokarin yin magudin zabe wannan hukunci nane kuma ba abinda zai faru ,” a cewar Abdullahi Abbas.
“Ina kira ga matasan jam’iyarmu da su tanadi makamansu a yanzu don akwai lokacin da za a yi amfani dasu.
Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano
Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”
Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye
Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.
Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.
Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa
Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.
Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.