KANUN LABARAI
Cin zarafi: Kotu ta umarci ‘yan sanda su binciki Baffa Babba Dan Agundi
Aminu Abdullahi
Kotun Majistire mai lamba 8 a Kano ta baiwa ‘yan sanda umarnin bincikar shugaban hukumar KAROTA Baffa Babba Dan Agundi bisa zargin cin zarafin wani matashi mai suna Mujitapha Isa.
Kano Focus ta ruwaito cewa lauyan Mujitiba, wato Abba Hikima Fagge ne ya shigar da korafin ga kotun yana kalubalantar Baffa Babba Dan Agundi da cin zarafi dan Adam.
A cewarsa hakan ya saba da doka musamman ma da ya raunata wanda yake karewa tare da yin kurin zai bashi cin hanci ga wanda ya casa din.
Barista Abba Hikima ya ce a ranar 25 ga watan Febrairun da ya gabata ne shugaban KAROTA ya lakadawa Mujitapha Isah duka, wanda har ta kai ga ya suma.

Baffan ya yi masa dukan kawo wukar ne bisa zargin yana daga cikin wadanda suka jagoranci zanga-zanga da kuma yajin aikin da direbobin Adai-daita Sahu suka yi a kwanakin baya.
Akwai ladan N150,000 ga wanda ya tona inda ake jabun magani a Kano- Baffa Babba
Zargin badakalar Tracker: Kotu ta ce a biya Bappa Babba N50,000 ladan bata masa lokaci
‘Yan Sahu don Allah ku yafemin kausasan kalamaina-Bappa Babba
“Sun kama shi bisa zargin raba takardu wanda suke zargin yana tunzura direbobin ne akan dokar harajin naira 100.
“Bayan kamashi ne bayan kwanaki uku da yajin aikin direbobin, sai aka kaishi gurin shugaban KAROTA Baffa Babba Dan Agundi a inda aka bayyana masa zargin.
“Sauraron zarginne kuma sai shugaban ya rufe wanda muke karewa da duka a sassa daban daban na jikin sa, da suka hada da wuya da kai da kuma kirjin sa,” a cewar sa.
Hikima ya ce daga nan ne aka dauke shi zuwa asibitin Murtala inda a nan ne ya farfado daga suman da yayi.
Ya ce bayan lura da sakamakon abin da ya aikata, sai ya kira mahaifin matashin tare da yi masa alkawarin aiki matukar yaki sanar da yan jarida ko kungiyoyi abinda ya faru.

Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
