Connect with us

Hausa

Inganta tsaro: Alfindiki ya samar da kofofin unguwannin masu kudi a cikin lokuna

Published

on

Aminu Abdullahi

Shugaban karamar hukumar Birni Fa’izu Alfindiki ya samar da wasu kofofi a lokuna da sakuna na wasu unguwanni a karamar hukumar Birni domin inganta tsaro.

A wani kewaye da Kano Focus ta gudanar, ta gano yadda aka samar da kofofin a unguwar Alfindiki, da Kwanar Goda, domin kulle lokunan idan dare yayi.

Wannan dai shi ne karo na farko da aka fara ganin irin wadannan kofofi na killace unguwanni a cikin birni, da galibin lokuta ana ganin irinsu ne kawai a unguwannin masu kudi.

A zantawar Kano Focus da wasu daga cikin mazauna unguwannin, su nuna jin dadin u da aikin da a ke yi musu, a cewarsu ko ba komai za a kara inganta tsaron yankin nasu.

Usman Balarabe mazaunin Alfinidiki ya ce a baya ba a saba ganin irin wadannan kofofi ba a unguwannin talakawa ko cikin birni.

Ya kara da cewa mafi a kasari layukan da ke unguwannin masu kudi ne ke samar da irin wadannan kofofi, tare da kullesu idan dare yayi.

“Wannan tsari ya yi sosai domin zai inganta tsaro a unguwanninmu, musamman a wannan lokaci da barayi kan haura gidajen al’umma da tsakar dare.

“Sannan kaga kowanne loko akwai wadanda aka dorawa alhakin rufe kofofinsa da zarar sha biyu na dare tayi,” a cewar sa.

Shima Musa Ibrahim mazaunin Kwanar Goda ya ce bai taba tunanin unguwanni irin nasu masu ginin kasa za su samu irin wannan cigabanba duba da cewa anfi samunsu a unguwannin masu hali.

“Daga lokacin da aka sanya mana wadannan kofofi ji nake tamkar muma ‘yan kasar waje ne,” a cewar sa.

Sai dai Bashir Muhammad Hassan ya ce samar da kofofin na da amfani, sai dai za su iya haddasa rikici a tsakanin makota.

Ya ce wasu magidanta basa komawa gidajensu da wuri sai bayan karfe goma sha biyu na dare.

“Idan kadawo katarar da kofar shiga lokon da gidan ka yake a rufe, kaga ai akwai matsala, kuma zaka iya kiran wayar wadanda mukullin gurin ke hannunsu a kashe.

“Ni ina ganin idan har kullewar ya zama dole to kowanne magidanci a bashi mukulli, ta yadda komin dare idan ya dawo zai iya budewa ya shiga,” a cewar sa.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Yunkurin tsige Malam Ibrahim Khalil wasan yara ne – Prof. Alkafawy

Published

on

Malam Ibrahim Khalil

Nasiru Yusuf

Majalisar Malamai ta Kasa ta bayyana yunkurin tsige Malam Ibrahim Khalil daga shugabancin Majalisar Malamai ta Jihar Kano da cewa wasan yara ne.

A wata sanarwa da KANO FOCUS ta samu Mai dauke da SA hannun Sakataren Kungiyar Farfesa Muhammad Sadik Alkafawy ya sanyawa hannu ranar Alhamis ta ce abun da aka yi ba ya bisa doka.

Ga cikakkiyar sanarwar:

“Majalisar  Malamai ta Kasa ta sami labarin yunkurin wata jama’a da ke kiran kanta Malamai, amma ta bari wasu wadanda ba su nufin alheri su yi amfani da su a kawo baraka tsakanin jama’ar Musulmi. Wannan abin takaici ne.

“Tun daga ranar da a ka assasa Majalisa zuwa yau ba a taba samun tabargaza irin wannan ba. Don haka Majalisa ta Kasa na yin kira ga wadannan mutane su tsoraci Allah su kauce ma son zuciya.

“Hakika Majalisar Malamai reshen jihar Kano ta yi daidai da tace wadanda su ka shiga wannan bankaura ba ‘ya’yanta ba ne tun daga jiha balle na Kasa. Yaya za a yi wanda ba ya cikin Majalisa ya ce ya kori wanda a ka kafa Majalisa da shi?.

“A wurin Majalisa ta Kasa abinda a ka yi ba ya bisa doka, kuma wasan yara ne. Hasali ma fata mu ke Allah ya ba shi shugabancinta na Kasa baki daya, amin.

“A karshe, Majalisar kasa ta yi mawafaka da duk abinda Majalisar Kano ta tsaya a Kai. Alhamdu Lillah.”

Continue Reading

Hausa

Tijjanawa ba sa goyon bayan nadin Pakistan shugaban Majalisar Malamai – Alkarmawi

Published

on

Khalifa Abdulmajid Alkarmawi

Khalifa Abdulmajid Alkarmawi

 

 

 

 

بسم الله الرحمن الرحيم 

وصلي الله علي النبي الكريم 

Majalisar Malamai ta jihar Kano tana da mahimmanci ga Musulmin Arewacin Nigeria gaba daya ba Kano ba kawai, don ko ba komai Al’ummar Musulmi suna kara samun hadin kai da magana da murya daya sanadiyar wannan majalisar kuma babban abun bukata shine hadin kan Musulmi.

Amma sabon shugabanci da akai jiya (Litinin) da aka nada Malam Abdallah Saleh Pakistan (Shugaban Izala na jahar kano) zai iya rusa majalisar ma gaba daya, Saboda Shugabancin yana bukatar malamin da yake Zaune lafiya da duk akidun Musulunci da suke Kano, wanda Pakistan kuwa yana da matsala da wasu bangarorin.

Shawarata kowa a nan shine Asami malamin da yaki da kyakkywar alaka da kowa ya jagoranci Alumma Sai asami kai wa ga gaci.

Don haka a madadin Tijjanawa, gaskiya gabadayanmu musamman na jihar Kano muna sanar da cewa ba ma tare da Shugabacin Malam Abdallah Saleh Pakistan.

Khalifa Abdulmajid Alkarmawi

Shugaban Khuddamur Rasul SAW na Afrika

Continue Reading

Hausa

Gamayyar Malaman Kano sun nesanta kan su daga tsige Malam Ibrahim Khalil

Published

on

Sheikh Ibrahim Khalil

Nasiru Yusuf

Gamayyar Malaman Jihar Kano da suka kunshi jagororin darikun Tijjaniyya da Qadiriyya da kuma Salafiyya sun yi watsi da sanarwar tsige Malam Ibrahim Khalil daga shugabancin majalisar malamai.

Wata sanarwa da KANO FOCUS ta ci karo da ita dauke da sa hannun sakataren gamayyar Malaman, Dr Sa’idu Ahmad Dukawa ranar Talata malaman sun ce ba da yawunsu aka dauki wannan mataki ba, kuma ba sa goyon bayansa.

Malaman da suka sahale a fitar da sanarwar sun hada da Shugaban Darikar Kadiriyya na Afrika ta Yamma Sheikh Karibullahi Sheikh Nasiru Kabara da Sheikh Abdulwahab Abdallah da Sheikh Ibrahim Sheh Maihula da Dr. Bashir Aliyu Umar da kuma Imam Nasir Muhammad Adam ( Shugaban majalisar Limaman masallatan Juma’a).

Sauran sun hada da Farfesa Musa Muhammad Borodo da Farfesa Muhammad Babangida da kuma Dr. Ibrahim Mu’azzam Maibushira.

Continue Reading

Trending