Connect with us

Hausa

Ramadan:Rahma Sadau ta tallafawa mabukata sama da 2000

Published

on

Aminu Abdullahi

Akalla mutane 2000 ne suka amfana da tallafin kayan abinci da jarumar fina-finan Hausa Rahma Sadau ta raba domin neman falalar azumin watan Ramadana.

Kano Focus ta ruwaito cewa a ranar Talata da Laraba da suka gabata ne jarumar ta kaddamar da rabon kayan abincin karkashin gidauniyar ta mai suna ‘Ray of Hope Foundation Africa’.

Jarumar ta yi rabon abincin ne a galibin wuraren da mabukata ke zama da suka hadar da Unguwar Rimi a jihar Kaduna da Hayin Na’iba da Birnin Yaro sai kuma Mararrabar Jos.

Wani makusancin jarumar Bello Sani Mada ya ce gidauniyar ta kwashe tsawon shekaru shida tana wannan aiki ba tare da ta bayyanawa  al’umma ba.

Haka zalika wannan kokari ya sa mutane da dama a shafukan sada zumunta ke cigaba da yabawa jarumar.

Alfaris Musa cewa ya yi yakamata al’umma su rinka kyautata zaton su ga abokan zaman su domin kuwa ko ba komai jarumar tafi wasu mutanen da yawa masu zagin ta.

“A cikin masu zagin ta za ka iya lissafa mutum hamsin da basu taba yin irin wannan taimakonba, kaga kuwa ko ba komai ai naka sai naka,” a cewar sa.

Ya kuma yi kira ga sauran jaruman Kannywood da suyi koyi da jarumar wajen yin abubuwan alkairi musamman na taimakawa mabukata.

Usman Balarabe ya ce kowanne mutum yana da nasa laifin amma sai ya take yazo kafar intanet a matsayin mai wa’azi.

Ya ce duk da irin abin kirkin da jarumar takeyi amma ba wanda yake yaba mata.

Amm amma da zarar an samu matsala guda sai kaga har wanda baya sallah akan lokaci shima wai ya zama mai wa’azi,” inji shi.

Idan za a iya tunawa dai al’umma a shafukan sada zumunta sun kalubalanci jarumar tare da yin Allah wadai kan wasu hotuna da ta wallafa a shafukanta da ta kai ga wani yayi batanci ga manzon Allah S.W.A.

Sai dai jarumar ta nemi afuwar al’ummar musulmi tare da alkawarin cewa ba za ta sake sanya makamancin hotunan ba

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Yunkurin tsige Malam Ibrahim Khalil wasan yara ne – Prof. Alkafawy

Published

on

Malam Ibrahim Khalil

Nasiru Yusuf

Majalisar Malamai ta Kasa ta bayyana yunkurin tsige Malam Ibrahim Khalil daga shugabancin Majalisar Malamai ta Jihar Kano da cewa wasan yara ne.

A wata sanarwa da KANO FOCUS ta samu Mai dauke da SA hannun Sakataren Kungiyar Farfesa Muhammad Sadik Alkafawy ya sanyawa hannu ranar Alhamis ta ce abun da aka yi ba ya bisa doka.

Ga cikakkiyar sanarwar:

“Majalisar  Malamai ta Kasa ta sami labarin yunkurin wata jama’a da ke kiran kanta Malamai, amma ta bari wasu wadanda ba su nufin alheri su yi amfani da su a kawo baraka tsakanin jama’ar Musulmi. Wannan abin takaici ne.

“Tun daga ranar da a ka assasa Majalisa zuwa yau ba a taba samun tabargaza irin wannan ba. Don haka Majalisa ta Kasa na yin kira ga wadannan mutane su tsoraci Allah su kauce ma son zuciya.

“Hakika Majalisar Malamai reshen jihar Kano ta yi daidai da tace wadanda su ka shiga wannan bankaura ba ‘ya’yanta ba ne tun daga jiha balle na Kasa. Yaya za a yi wanda ba ya cikin Majalisa ya ce ya kori wanda a ka kafa Majalisa da shi?.

“A wurin Majalisa ta Kasa abinda a ka yi ba ya bisa doka, kuma wasan yara ne. Hasali ma fata mu ke Allah ya ba shi shugabancinta na Kasa baki daya, amin.

“A karshe, Majalisar kasa ta yi mawafaka da duk abinda Majalisar Kano ta tsaya a Kai. Alhamdu Lillah.”

Continue Reading

Hausa

Tijjanawa ba sa goyon bayan nadin Pakistan shugaban Majalisar Malamai – Alkarmawi

Published

on

Khalifa Abdulmajid Alkarmawi

Khalifa Abdulmajid Alkarmawi

 

 

 

 

بسم الله الرحمن الرحيم 

وصلي الله علي النبي الكريم 

Majalisar Malamai ta jihar Kano tana da mahimmanci ga Musulmin Arewacin Nigeria gaba daya ba Kano ba kawai, don ko ba komai Al’ummar Musulmi suna kara samun hadin kai da magana da murya daya sanadiyar wannan majalisar kuma babban abun bukata shine hadin kan Musulmi.

Amma sabon shugabanci da akai jiya (Litinin) da aka nada Malam Abdallah Saleh Pakistan (Shugaban Izala na jahar kano) zai iya rusa majalisar ma gaba daya, Saboda Shugabancin yana bukatar malamin da yake Zaune lafiya da duk akidun Musulunci da suke Kano, wanda Pakistan kuwa yana da matsala da wasu bangarorin.

Shawarata kowa a nan shine Asami malamin da yaki da kyakkywar alaka da kowa ya jagoranci Alumma Sai asami kai wa ga gaci.

Don haka a madadin Tijjanawa, gaskiya gabadayanmu musamman na jihar Kano muna sanar da cewa ba ma tare da Shugabacin Malam Abdallah Saleh Pakistan.

Khalifa Abdulmajid Alkarmawi

Shugaban Khuddamur Rasul SAW na Afrika

Continue Reading

Hausa

Gamayyar Malaman Kano sun nesanta kan su daga tsige Malam Ibrahim Khalil

Published

on

Sheikh Ibrahim Khalil

Nasiru Yusuf

Gamayyar Malaman Jihar Kano da suka kunshi jagororin darikun Tijjaniyya da Qadiriyya da kuma Salafiyya sun yi watsi da sanarwar tsige Malam Ibrahim Khalil daga shugabancin majalisar malamai.

Wata sanarwa da KANO FOCUS ta ci karo da ita dauke da sa hannun sakataren gamayyar Malaman, Dr Sa’idu Ahmad Dukawa ranar Talata malaman sun ce ba da yawunsu aka dauki wannan mataki ba, kuma ba sa goyon bayansa.

Malaman da suka sahale a fitar da sanarwar sun hada da Shugaban Darikar Kadiriyya na Afrika ta Yamma Sheikh Karibullahi Sheikh Nasiru Kabara da Sheikh Abdulwahab Abdallah da Sheikh Ibrahim Sheh Maihula da Dr. Bashir Aliyu Umar da kuma Imam Nasir Muhammad Adam ( Shugaban majalisar Limaman masallatan Juma’a).

Sauran sun hada da Farfesa Musa Muhammad Borodo da Farfesa Muhammad Babangida da kuma Dr. Ibrahim Mu’azzam Maibushira.

Continue Reading

Trending