Connect with us

Hausa

Yadda aikin titin Dandishe ke shirin hallaka al’ummar yankin

Published

on

Aminu Abdullahi

Al’ummar Unguwar Dandishe da ke karamar hukumar Dala a nan Kano sunce suna kamuwa da cutuka iri-iri da suka hadar da Athma, sakamakon kwazazzabon da aka haka musu da sunan gyaran titi.

Haka zalika sun ce matansu na yin bari, ko kuma su haihu nan take da zarar an dauke su zuwa asibiti saboda rashin kyawun hanyar.

A wani bincike da jaridar Kano Focus ta gudanar ta gano yadda aikin ginin titin da ya tashi daga Dandishe, zuwa  Gobirawa yabi ta Tudun Fulani ya bulle a Bachirawa ya zame musu jangwam.

A cewar al’ummar yankin ginin titin na haifarmusu da cutuka da dama wadanda a da basu da su da suka hadar da Asthma, mura mai zafi da wasu cutuka da har yazu ba su kai ga gano su ba.

Haka zalika sun ce da wuya a dauko mace mai juna biyu da ga farkon titin zuwa karshensa, bata zubar da cikinba ko kuma ta haihu a kan hayar.

Annur Ahmad Muhammad wani mai yin sana’a ne a gefen titin, ya ce an dawo da aikin titin ba da jimawaba, kwatsam sai aka nemi masu aikin aka rasa.

Ya ce matafiya da wadanda ke sana’a a gurin nashan wahala, da hakan yasa masu cutar asma ke tashi a duk lokacin da suke tafiya a titin.

Umar Ashir Alhassan cewa ya yi basu ji dadin yadda gwamnati ta tsaida aikin ba.

Ya ce wasu lokutan mata kanyi bari, ya yin da ake kaisu asibiti sakamakon lalacewar da hanyar tayi.

Ya kara da cewa gyara titin zai saukaka yawan cunkoso da ake samu a babban titin kurna.

Da gangan gwamnati ta tsayar da aikin

Haka zalika al’ummar yankin sun zargi gwamnatin Kano da tsayar da aikin da gangan.

Acewarsu dan kwangilar dake aikin titin ya kwashe motoci da kayayyakin aikin a makonnin da suka gabata.

Titin na Dandishe mai tsahon kilomita shida ya shafe shekaru biyar a lalace har yanzu kuma an kasa kammala shi

Idan za a iya tunawa dai a karshen shekarar 2020 ne akadawo da aikin gyaran titin kafin daga bisani a farkon shekarar 2021 dan kwangilar ya kwashe kayan sa.

Ko da yake wasu majiyoyi sun ce rashin biyan dankwangilar hakkokin sa da gwamnatin tayi ne yasa ya dakatar da aikin.

Ba mu san dan kwangilar ya gudu ba

Ko da Kano Focus ta tuntubi kwamishinan ayyuka na jihar Kano  Idris Garba Unguwar Rimi ya ce basu da masaniyar dakatar da aikin.

Unguwar Rimi ya ce basu san dan kwangilar ya dakatar da aikin titin ba.

A cewarsa sunyi yarjejeniya kan cewa za a kammala aikin kafin lokacin damina.

Ya kara da cewa zai gayyaci dankwangilar domin jin dalilin dakatar da aikin ginin titin.

Ya kuma baiwa al’ummar yankin hakura, acewarsa za su tabbatar an kammala aikin kafin zuwan lokacin damina.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Yunkurin tsige Malam Ibrahim Khalil wasan yara ne – Prof. Alkafawy

Published

on

Malam Ibrahim Khalil

Nasiru Yusuf

Majalisar Malamai ta Kasa ta bayyana yunkurin tsige Malam Ibrahim Khalil daga shugabancin Majalisar Malamai ta Jihar Kano da cewa wasan yara ne.

A wata sanarwa da KANO FOCUS ta samu Mai dauke da SA hannun Sakataren Kungiyar Farfesa Muhammad Sadik Alkafawy ya sanyawa hannu ranar Alhamis ta ce abun da aka yi ba ya bisa doka.

Ga cikakkiyar sanarwar:

“Majalisar  Malamai ta Kasa ta sami labarin yunkurin wata jama’a da ke kiran kanta Malamai, amma ta bari wasu wadanda ba su nufin alheri su yi amfani da su a kawo baraka tsakanin jama’ar Musulmi. Wannan abin takaici ne.

“Tun daga ranar da a ka assasa Majalisa zuwa yau ba a taba samun tabargaza irin wannan ba. Don haka Majalisa ta Kasa na yin kira ga wadannan mutane su tsoraci Allah su kauce ma son zuciya.

“Hakika Majalisar Malamai reshen jihar Kano ta yi daidai da tace wadanda su ka shiga wannan bankaura ba ‘ya’yanta ba ne tun daga jiha balle na Kasa. Yaya za a yi wanda ba ya cikin Majalisa ya ce ya kori wanda a ka kafa Majalisa da shi?.

“A wurin Majalisa ta Kasa abinda a ka yi ba ya bisa doka, kuma wasan yara ne. Hasali ma fata mu ke Allah ya ba shi shugabancinta na Kasa baki daya, amin.

“A karshe, Majalisar kasa ta yi mawafaka da duk abinda Majalisar Kano ta tsaya a Kai. Alhamdu Lillah.”

Continue Reading

Hausa

Tijjanawa ba sa goyon bayan nadin Pakistan shugaban Majalisar Malamai – Alkarmawi

Published

on

Khalifa Abdulmajid Alkarmawi

Khalifa Abdulmajid Alkarmawi

 

 

 

 

بسم الله الرحمن الرحيم 

وصلي الله علي النبي الكريم 

Majalisar Malamai ta jihar Kano tana da mahimmanci ga Musulmin Arewacin Nigeria gaba daya ba Kano ba kawai, don ko ba komai Al’ummar Musulmi suna kara samun hadin kai da magana da murya daya sanadiyar wannan majalisar kuma babban abun bukata shine hadin kan Musulmi.

Amma sabon shugabanci da akai jiya (Litinin) da aka nada Malam Abdallah Saleh Pakistan (Shugaban Izala na jahar kano) zai iya rusa majalisar ma gaba daya, Saboda Shugabancin yana bukatar malamin da yake Zaune lafiya da duk akidun Musulunci da suke Kano, wanda Pakistan kuwa yana da matsala da wasu bangarorin.

Shawarata kowa a nan shine Asami malamin da yaki da kyakkywar alaka da kowa ya jagoranci Alumma Sai asami kai wa ga gaci.

Don haka a madadin Tijjanawa, gaskiya gabadayanmu musamman na jihar Kano muna sanar da cewa ba ma tare da Shugabacin Malam Abdallah Saleh Pakistan.

Khalifa Abdulmajid Alkarmawi

Shugaban Khuddamur Rasul SAW na Afrika

Continue Reading

Hausa

Gamayyar Malaman Kano sun nesanta kan su daga tsige Malam Ibrahim Khalil

Published

on

Sheikh Ibrahim Khalil

Nasiru Yusuf

Gamayyar Malaman Jihar Kano da suka kunshi jagororin darikun Tijjaniyya da Qadiriyya da kuma Salafiyya sun yi watsi da sanarwar tsige Malam Ibrahim Khalil daga shugabancin majalisar malamai.

Wata sanarwa da KANO FOCUS ta ci karo da ita dauke da sa hannun sakataren gamayyar Malaman, Dr Sa’idu Ahmad Dukawa ranar Talata malaman sun ce ba da yawunsu aka dauki wannan mataki ba, kuma ba sa goyon bayansa.

Malaman da suka sahale a fitar da sanarwar sun hada da Shugaban Darikar Kadiriyya na Afrika ta Yamma Sheikh Karibullahi Sheikh Nasiru Kabara da Sheikh Abdulwahab Abdallah da Sheikh Ibrahim Sheh Maihula da Dr. Bashir Aliyu Umar da kuma Imam Nasir Muhammad Adam ( Shugaban majalisar Limaman masallatan Juma’a).

Sauran sun hada da Farfesa Musa Muhammad Borodo da Farfesa Muhammad Babangida da kuma Dr. Ibrahim Mu’azzam Maibushira.

Continue Reading

Trending