Connect with us

Hausa

Yunkurin raba kan ‘Yan Darikar Tijjaniyyah, saboda hassadar da suke yi wa Mai Martaba Sarkin Kano Khalifah Malam Muhammadu Sanusi II

Published

on

Sheikh Sherif Ibrahim Saleh da Khalifa Muhammadu Sanusi ll

Daga Imam Murtadha Gusau

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai

Assalamu Alaikum

Ya ku bayin Allah! Abu ne da kowa ya sani, kuma ya amince, kuma babu wata jayayya akai, cewa hadin kan Musulmi wajibi ne, kuma rabuwa sharri ne, azaba ne kuma bala’i ne. Allah da Manzonsa (SAW) sun umurci Musulmi da su hada kan su. Kuma suka tabbatar masu da cewa, hadin kan nan shine sharadin zaman lafiyar su da ci gaban su. Idan Musulmi sun hada kai, zasu rabauta duniya da lahira. Idan kuwa suka rarrabu, suka ki bin umurnin Allah da Manzonsa, to lallai, tun anan duniya zasu ga mummunan sakamakon aikin su, kafin su tafi lahira, su hadu da Allah mahaliccin su.

Ya ku bayin Allah, wannan hadin kai da Allah da Manzonsa (SAW) suka yi umurni, shine Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje yake kokarin rusawa, da sunan yakar Mai Martaba Sarkin Kano Khalifah Malam Muhammadu Sanusi II, sanadiyyar hasadar da yake nuna masa, kuma wadda taki-ci-taki-cinyewa!

Abu ne da yake a fili karara cewa, tun lokacin da aka nada Mai Martaba Sarkin Kano Khalifah Malam Muhammadu Sanusi II a matsayin Khalifan Tijjaniyyah a Najeriya, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje bai yi kasa a gwiwa ba wurin yakar sa, kamar yadda yake ta yakar sa a can baya, saboda Sarkin ya dage akan cewa, dole ne ayi gaskiya.

Wallahi ba yadda Gwamna Ganduje bai yi ba na ganin cewa ya hana ayi nadin, to amma da yake duk abun da Allah yayi, dan Adam ba ya iya hanawa, sai da Allah Subhanahu wa Ta’ala ya tabbatar da wannan mukami na Khalifanci ga Khalifah Muhammadu Sanusi II.

Bayan da Gwamna Ganduje ya kasa soke nadin Khalifancin, sai ya yanke shawarar cewa bari yabi wata hanyar da duk zai bi, domin dai ya kawowa Sarki Muhammadu Sanusi II matsala. Sanadiyyar haka, sai ya dauki Ibrahim Dahiru Bauchi da Isa Sanusi Bayero (Isa Pilot) domin suyi aiki tare da shi, na ganin ya cimma wannan bakin buri nasa.

Gwamna Ganduje da wadannan mutane, sun yi yunkuri a lokuta daban-daban domin gudanar da zaman Zikiri a masarautar Kano, wanda wai a nasu tunanin, zai zama taron da ba’a taba yin irin sa ba a tarihin masarautar, amma duk basu ci nasara ba. Sai wannan karon kuma basu gajiya ba, suka shirya wani taron na Zikiri, wanda zai kalubalanci taron da aka shirya na duniya a garin Lokoja, domin gudanar da Maulidi tare da yiwa kasa addu’o’in zaman lafiya da samun ci gaba da hadin kai mai dorewa.

Ganduje da mutanen nasa, suna ganin cewa, su a irin nasu fahimtar, idan suka kira wannan taro a Kano, kuma suka sanya shi rana daya da wanda za’a yi a garin Lokoja, to lallai tabbas taron na Lokoja zai hadu da cikas. Kuma idan hakan ya faru, to sun cimma burin su, kuma sun kunyata Mai Martaba Sarkin Kano Khalifah Malam Muhammadu Sanusi II a idon duniya.

Amma da yake Allah baya zalunci, kuma ya haramtawa kansa zalunci, kuma ya hane mu da yin zalunci, kuma ya tabbatar muna da cewa, tabbas zai ci gaba da kunyata dukkan wani mutum azzalumi a duk inda yake, sai aka wayi gari yunkurin nasu ya hadu da cikas, kuma ya hadu da matsala.

Hakan ya faru ne saboda dukkanin Shehunan darikar Tijjaniyyah na Kano da sauran wurare, sun nuna cewa su fa suna tare da Sarki Muhammadu Sanusi II, kuma sun nuna cewa darikar Tijjaniyyah ba wata haja bace ta sayarwa, bare wani dan siyasa ya saye su da kudi. Sun nuna dattako, kuma sun yanke shawarar kaucewa duk wani abu da ya shafi yunkurin Gwamna Ganduje na zagon kasa ga darikar Tijjaniyyah da Khalifah Muhammadu Sanusi II.

Dukkanin Shehunnai da Khalifofin darikar Tijjaniyyah a Najeriya, sun fahimci abun da yake faruwa na yunkurin raba kawunan su, da kuma tarwatsasu da Gwamna Ganduje yake kokarin yi.

Ya ku bayin Allah! Wallahi wannan matsayi na kafatanin Shehunnan darikar Tijjaniyyah, ya kara jawo masu daraja da matsayi a idon duniya. Domin anyi yunkurin yin amfani da kudi, da kuma karfin gwamnati, amma suka kafe, suka ki yarda, suka zabi su kasance tare da gaskiya, da kuma masu gaskiya.

Kai yanzu ma su Shehunnan darikar Tijjaniyyah, yanzu sun gano wani yunkuri, da wata makarkashiya, na kokarin samar da wata kishiya da zata kalubalanci jagorancin Darikar Tijjaniyyah na duniya baki daya. Shi yasa aka dauki nauyin zuwa kasar Algeria, a dauko Shehunnai can, domin jagorancin da yake a kasar Senegal a yanzu, an kasa sayen su da kudi. Don haka, tun da basu mika wuya ba, to bari a manta da su, ayi hulda da Shehunnan kasar Algeria.

Shi yasa Gwamna Ganduje ya dauki nauyin ziyarar Ibrahim Dahiru Bauchi zuwa kasar Aljeriya akan ya gayyato wani Shugaban Darikar Tijjaniyyah, da sauran Shehunnai da Malamai, domin suzo Kano, domin yin Zikiri a ranar Juma’ah, 7 ga watan Janairun 2022, wai duk domin a dakile wancan muhimmin Zikirin da taron yiwa kasa addu’a, da za’a yi a garin Lokoja, babban birnin jihar Kogi, wato a rana makamanciyarta, wanda gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Adoza Bello, ya roka ayi, kuma ya shirya a garin na Lokaja, kuma taron da Mai Martaba Sarkin Kano Khalifah Malam Muhammadu Sanusi II ne zai jagorance shi.

Majalisar Shura ta Darikar Tijjaniyyah ta koli ta jihar Kano, kakashin jagorancin Sheikh Abdullahi Uwais Limanci, ta yanke shawarar cewa babu ruwanta da duk wani abu na shirin raba kan al’ummah da Gwamna Ganduje  yake son yi.

Idan dai har al’ummar kasar nan zasu iya tunawa, a can baya, Gwamna Ganduje ya bayyana Shehunan Darikar Tijjaniyyah, a matsayin wadanda ba zasu iya tabuka komai ba, domin ceto sarautar Mai Martaba Sarkin Kano Khalifah Malam Muhammdu Sanusi II, a inda yace duk addu’ar da suke yi ba zata yi amfani ba, domin wai “SUN KAMA KAFAR WALA”!

To yanzu dai alhamdulillahi, domin duniya ta yabawa Shehunan Darikar Tijjaniyyah na Kano, da na Najeriya baki daya, saboda sun nuna wa Gwamna Ganduje cewa su ba za’a iya sayen su da kudi ba. Dukkanin su sun yanke shawarar halartar babban taron da za’a yi a garin Lokoja, tare da wakilai daga Kaulaha da kasar Maroko. Kuma alhamdulillahi, galibin mabiya Darikar Tijjaniyyah a Najeriya, sunyi mubaya’ah ga jagorancin Mai Martaba Sarkin Kano Khalifah Malam Muhammadu Sanusi II, a matsayin shugaba daya tilo da Kaulaha da Maroko suka amince da shi.

Kuma alhamdulillahi, yanzu dai ta tabbata cewa, Gwamna Ganduje ya gaza a wurin yakar Darikar Tijjaniyyah, kamar yadda kuma ya gaza a wurin yakar Majalisar Malamai ta jihar Kano, a lokacin da yayi yunkurin tsige Malam Ibrahim Khalil saboda tsananin rashin kunya.

Kamar yadda kuka sani, Gwamna Ganduje da ‘yan kanzagin nasa, sun gayyaci dukkanin Shugabannin Darikar Tijjaniyyah na kasar Senegal, domin su halarci taron na Kano, amma shugabannin sunce sam ba zasu zo ba, domin ba zasu taba bayar da goyon baya akan abun da duk zai raba kan jama’ar su ba.

Ganin cewa Ibrahim Dahiru Bauchi ya kasa shawo kansu, shi ne sai aka tayar da jirgi na musamman, tare da su Isa Pilot, domin a dauki Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya tafi Senegal, domin a lallashi shugabannin darikar su amince suzo. Amma duk lallashin da aka yi, sun ce sam ba zasu zo Zikirin na Kano ba. To shine, suka samu wasu samari, matasa, daga kasar Senegal din, suka zo da su, domin su halarci taron na Kano, da sunan wai wakilan shugabannin. Idan hakan ya kasance, to wai su a ganin su, basu kunyata ba!

A can baya idan kun tuna, Gwamna Ganduje yayi amfani da wasu bara-gurbi, marasa kishi, ya samu nasarar ruguza Masarautar Kano mai tarin albarka, mai dimbin tarihi, mai cike da kima da kwarjini, wanda a halin yanzu ya mayar da Masarautar wani dandali na shiririta, ta hanyar zalunci.

Da ikon Allah, muna nan muna ta addu’a da rokon Allah, da fatan Allah ya kawo wa Kanawa da jihar Kano adalin Gwamna, wanda zai dawowa da jihar Kano, da kuma Masarautar Kano da kwarjinin nan nasu da Allah ya basu, kuma da ikon Allah, ya gyara dukkanin barnar da Gwamna Ganduje yayiwa jihar!

Sannan ina mai tabbatar maku da cewa, Gwamna Ganduje da duk ‘yan kanzagin nasa, ba zasu taba cin nasara a dukkan wani mummunan tanadi, da wani yunkurin sharri nasu ba. Kuma zasu ci gaba da takaicin abin da ya shafi Mai Martaba Sarkin Kano Khalifah Malam Muhammadu Sanusi II; domin shi Sarki Muhammadu Sanusi II wallahi yin Allah ne, ba yin kansa bane. Kuma liyafah da karramawa da aka yi masa kwanan nan a kasar Ghana, shaida ce dake nuna matsayinsa da daukakar darajarsa.

Kuma a daya gefen, ya kamata Gwamna Ganduje ya san da cewa, ikonsa da mulkinsa ba zasu iya tsallakawa zuwa ko’ina a Najeriya a fadin Najeriya ba, idan ba Kano kawai ba. Amma ikon Mai Martaba Sarkin Kano Khalifah Malam Muhammadu Sanusi II, wanda yake yiwa hassada, wallahi ya wuce nahiyar Afirka, ya shiga duniya ko’ina. Wannan kuwa daga Allah ne.

Daga karshe, muna sanar da jama’ah cewa, bayan taron Zikiri da yi wa kasa addu’a, da aka saba gabatarwa a Masarautar Kano tare da Shehunnan darikar Tijjaniyyah, wato wanda ake gabatarwa a watan Muharram sau daya a shekara, bamu san da wani taron Zikirin da wasu suka shirya domin raba kan jama’ah ba. Muna kira, da ku kauracewa duk wata sanarwar gayyatar Zikiri da ake yadawa, wai za’a yi a Kano. Duk wani taro da bai sami izinin Khalifofin Shehu ba, kada su halarce shi. Dukkanin Shehunnai ba zasu halarta ba. Taron Lokoja shine halattacen taro. Idan kana da iko can zaka je. Idan kuwa babu halin zuwa, to ana kira ga ‘yan uwa da su zauna a zawiyoyinsu suyi Zikiri.

Kuma mun samu tabbataccen labari cewa an dauki nauyin ‘yan jagaliya, da wasu ‘yan kungiyoyi, da zauna-gari-banza, za’a biya su makudan kudade, domin su halarci taron da aka shirya a Kano din domin raba kan jama’ah. Wai da nufin su nunawa duniya cewa, sun shirya taron Zikiri, kuma an amsa kira. Don haka jama’ah, ayi hankali!

Alhamdulillah, a yau din nan, kuma a yanzun nan, da karfe biyar daidai (5:00 pm) na yammacin ranar alhamis, 06/01/2022, da ni ke wannan rubutu, domin sanar da duniya hakikanin halin da ake ciki, domin kar su yarda a rude su karyar banza, Mai Martaba Sarkin Kano Khalifah Malam Muhammadu Sanusi II, shi da tawagarsa, da sauran Khalifofi, da Shehunnai da mukadamai, kai da duk wani mai fada aji a cikin Darikar Tijjaniyyah, a Najeriya da kewaye, duk sun sauka, sun halara a garin Lokoja.

Kuma yanzu ana tsakiyar cigaba da shirye-shiryen gabatar da Maulidi da Zikiri da yiwa kasa addu’a da rokon Allah na musamman, a garin na Lokoja, jihar Kogi.

Sannan ya ku bayin Allah! Ya ku masoya Mai Martaba Sarkin Kano Khalifah Malam Muhammadu Sanusi II, ku sani, wallahi lokaci yayi da ya kamata mu nuna kishin mu tsantsa akan Khalifah Muhammadu Sanusi II. Ku sani, duk wannan kiyayyar da ake nunawa Khalifah Muhammadu Sanusi II ba komai bane illa tsantsar hassada, kiyayya da gaba. Hakan kuma bai samu ba sai da hadin kan Gwamnati, da kuma wasu bara-gurbi. Don haka, ya kamata soyayyar mu ta zama a zahirance, a aikace, zuwa ga Khalifah, ba wai a hoto kawai, ko a baki ba. Ya zama dole, kuma tilas, mu nuna, ta kowane hali, cewa, muna tare da Mai Martaba Khalifah Muhammadu Sanusi II.

Ina addu’a da rokon Allah ya karawa Khalifah lafiya, imani da nisan kwana; kuma Allah yasa ya ga bayan dukkanin makiyansa, amin.

Wassalamu alaikum,

Dan uwan ku: Imam Murtadha Muhammad Gusau ne ya rubuta, daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa ta lambar waya kamar haka: 08038289761.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Hausa

Pantami ya ziyarci iyayen Hanifa Abubakar

Published

on

Nasiru Yusuf

Ministan Sadarwa Farfesa Isa Ali Pantami ya kai ziyarar ta’aziyya gidan su Hanifa Abubakar, yarinya ‘yar shekara biyar waddaa aka kama shugaban makarantarsu da laifin yi mata kisan gilla.

KANO FOCUS ta ruwaito cewa Pantami ya yi ta’aziyya ga mahaifin yarinya, Malam Abubakar, inda daga bisani mahaifin yarinyar ya jagoranci Minista shiga  cikin gida don yi wa mahaifiyar Hanifa da yan’uwanta ta’aziyya da nasihohi.

Malam Pantami ya yi nasiha ga iyayen Hanifa akan wajibcin hakuri lokacin jarrabawa mai tsanani irin wannan.

Farfesa Pantami, ya roki Allah Ya sanya marigayiya Hanifa Abubakar ta zama mai ceto a lahira ga iyayenta, ya kuma bawa iyayen hakuri akan wannan babban rashi da ya faru sanadiyar wasu azzalumai da suka nuna rashin imani.

Iyayen marigayiya Hanifa Abubakar sun godewa Malam da adduar fatan alheri akan nasihohi da addu’o’i da ya gabatar.

Continue Reading

Hausa

KAROTA ta rage kudin shaidar tuka Adaidata Sahu daga 8000 zuwa 5000

Published

on

Adaidaita Sahu

Mukhtar Yahya Usman

Hukumar KAROTA ta ragewa ‘yan Adaidata Sahu kudin sabunta shaidar tuki daga dubu N8000 zuwa N5000.

KANO FOCUS ta ruwaito wannan na kunshe cikin wata sanarwar da jami’in hulda da jama’a na hukumar Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa ya fitar ranar Laraba.

Sanarwar ta ce hukumar ta kuma rage kudin rijistar sabuwar shaidar tukin daga 18,000 zuwa N1500.

Wannan ya biyo bayan zaman sulhun da aka yi tsakanin hukumar ta KAROTA da lauyoyin ‘yan Adaidata Sahu a shelkwatar kungiyar lauyoyi ta jihar Kano.

Zaman ya guda na ne ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙungiyar Lauyoyi na jihar Kano Barista Aminu Sani Gadanya.

Ya yin zaman an comma matsala kan dukkan dan Sahu zai biya kudin nan da karshen watan Fabrairu mai kamawa.

Haka kuma an amince duk dan Sahun da ya Gaza biya har wa’adin ya cika to zai biya a tsarin kudin baya.

Zaman ya kuma amince da biyan harajin kulum-kullum ciki har da Lahadi wadda aka dauke musu a baya.

Da yake jawabi Jim Kadan bayan kammala zaman shugaban hukar KAROTA Baffa Babba Dan Agundi ya ce Hukumar da matuka Baburan adaidaita sahun sun sami kyakkyawar fahimtar juna a lokacin da suke gudanar da tuƙi a kan titi.

Continue Reading

Hausa

FG appoints Sa’a Ibrahim, Kankarofi members of audience measurement task force

Published

on

Nasiru Yusuf

The Minister of Information and Culture, Alhaji Lai Mohammed has on Tuesday inaugurated  a 15-member audience measurement task force, which has Director General of Abubakar Rimi Television Sa’a Ibrahim and Garba Bello Kankarofi as members.

KANO FOCUS reports that Sa’a Ibrahim is the immediate past chairperson of Broadcasting Organization of Nigeria (BON) while Kankarofi is the former registrar of Advertising Practitioners Council of Nigeria (APCON).

The Task Force has Tolu Ogunkoya as Chairman with Femi Adelusi, Steve Babaeko, Bunmi Adeniba, and Jibe Ologe as members.

Others are Yinka Oduniyi, Guy Murray Bruce, Ms Kadaria Ahmed, Pauline Ehusani, Ijedi Iyoha, Mahmoud Ali-Balogun, Obi Asika and Joe Mutah (Secretary).

Speaking at the occasion Lai Muhammad said putting in place a scientific audience measurement system would boost investments in Nigeria’s broadcast and advertising industries.

He said, “We are committed to delivering an empirical audience measure system that will catalyze investment in broadcast and advertising industries, ensure the success of the DSO project as well as fire the imagination and boost the morale of creatives.

“We are undaunted by the enormity of the challenges we face in this regard, because we have a bunch of committed, patriotic and hardworking men and women to tackle the challenges headlong.”

Mohammed said the inauguration was the culmination of a series of events that included the setting up of the Task Team on Audience Measurement and the selection of First Media and Entertainment Integrated (Nigeria) Limited, a marketing research company based in Lagos, to deliver audience measurement services in Nigeria.

The Minister said the absence of a scientific audience measurement system has resulted in under-development in the broadcast and advertising industries and stunted their growth.

“Nigeria’s broadcast advertising market is punching far below its weight, especially when the country’s population is taken into account. Despite having a population more than three times that of South Africa, Nigeria’s television advertising market revenue in 2016 was $309 million, compared to that of South Africa, which was S$1.3 billion. Nigeria’s broadcast advertising market is also third in Africa, behind that of South Africa and Kenya.

“The immediate challenge before us, therefore, is to bring the under-performing Nigeria TV and radio advertising market to what it should be – which is two or three times what it is now. If we do that, it could result in additional $400 million revenue or more in the industry in the next three years.”

The Minister said a scientific audience measurement system was also critical to the success of the DSO.

“The existing model will never allow Nigeria’s Creative Industry to reach its full potential. It stunts the quality of the content that can be created and also limits the capacity of television platforms to invest in dynamic contents that consumers will be attracted to,” Mohammed said.

He charged the task force to Identify best practice audience measurement system that will support the sustainable growth of the Nigerian creative and entertainment industry; supervise the established framework for supporting the sustainability of the audience measurement system, independent of the Federal Government; and recommend a payment and disbursement framework among the key stakeholders in the industry, that is Broadcasting Organisations of Nigeria Media Independent Practitioners Association of Nigeria and Advertisers Association of Nigeria.

The Minister also challenged the task force to urgently grow the Nigerian television advertisement market to two or three times its current size.

In his response, Ogunkoya, promised that his panel would take the charge by the Minister very seriously, adding: “If we get this right, we would have done the industry and the nation proud.

Continue Reading

Trending