Connect with us

Hausa

Waiwaye kan Gasar Kofin Nahiyar Afrika (AFCON)

Published

on

Jamilu Uba Adamu

A yau ne aka fara wasannin gasar Kwallon Kafa ta kasashen Nahiyar Afrika a kasar Kamaru.

Bisa hakane naga dacewar yin waiwaye akan gasar, musamman akan Kasata Najeriya.

Gasar kofin cin zakarun nahiyar Afrika ta farko an yi ta ne a kasar Sudan a yayin kafa tarayyar hukumar kwallon kafa ta Afrika a babban birnin Khartoum a shekarar 1957.

Sai dai a shekarar da aka fara gasar 1957 kamar yadda tarihi ya nuna, an fara gasar ne da kasashe uku rak,  kasancewar mafi yawan kasashen Africa na karkashin mulkin mallaka (Don a wancan zamanin, kokarin karbar mulkin yancin kai ake bata Kwallon kafa ba ).

Kasar Afrika ta Kudu wadda na cikin kasashen da aka kirkiri gasar da ita lokacin tana karkashin mulkin masu nuna wariyar launin fata (Apartheid) an hanata shiga gasar bisa dalilin nuna kin jinin bakar fata (saboda ba su yarda asa bakin fata a Kungiyar da zata wakilci kasar tasu ba).

Don haka a gasar ta farko an ba wa Kasar Ethiopia damar shiga rukunin wasan karshe kyauta, inda aka fafata wasan wasan kusa da na karshe tsakanin Kasar Egypt da Kasar Sudan. Egypt ce ta yi nasara a wasan da ci 2-1 akan masu masaukin baki Sudan.

A wasan Karshe Kasar Egypt ta lashe gasar ta nahiyar Afrika  karo na farko da aka fara bayan ta lallasa Kasar ta Ethiopia da ci 4-0.

A shekarar 1962 ne aka fara samun yawan kasashen da suka samu yancin kai daga Turawan mulkin mallaka, wanda yawan kasashen dake san shiga gasar yayi yawa dan haka hukumar kwallon kafa Afrika (CAF) ta fito da tsarin yin wasan share fage (Qualifying Rounds). A wannan shekarun ne kasar Ghana ta samu nasarar lashe gasannin Shekaraun 1963 da 1965 a jere.

A kusan koda yaushe ana daukar Najeriya a matsayin daya daga cikin kasashen da ka iya lashe kofin wannan gasar.

Saboda Kungiyar Kwallon kafa ta Kasa Najeriya Super Eagles na da tarihi mai yawa a wannnan gasa ta cin kofin kwallon kafa na kasashen Afrika.

A yadda tarihi ya nuna Najeriya tafi shan wahala a wajen buga wasannin share fagen shiga gasar, amma suna kokarin kai mataki mai nisa indai sun haye matakin rukunin share fage.

A shekarun 1965-1970 Najeriya ta fita daga gasar saboda yakin basasa da ta yi fama da shi. Hakazalika a shekarar 1996 sun janye daga gasar wadda aka shirya a kasar Afrika ta kudu. Najeriya Bata Samu hayewa daga wasannin share fagge ba na shekarun 2012,2015 da 2017 ba.

Kungiyar Kwallon kafar Najeriya ta fara Zama zakara a wanann gasa ne a shekarar 1980 Wanda aka shirya a Gida Najeriya. A wasan karshe Wanda aka yi a birnin Ikko Najeriya ta Lallasa kasar Aljeriya da ci Uku da nema 3-0.

Najeriya ta sake lashe kofin a shekarar 1994 bayan Lallasa kasar Zambia da ci biyu da nema 2-1.

A shekarar 2013 an shirya gasar a Afrika ta Kudu Kuma Najeriya ce ta lashe gasar, a wasan karshe sun buge kasar Burkina Faso da ci daya da nema ( 1-0 )

Najeriya tayi Rashin Nasara a wasan Karshe ( Final ) har sau Hudu a shekarun 1984,1988, 1990 da 2000.Inda ta Kare a matsayin na Biyu kenan.

Ta kuma kare a matsayi na uku a gasar,  har sau takwas a shekarun 1976, 1978, 1992, 2002, 2004, 2006, 2010 da 2019.

Wannan tarihin da Najeriya take da shi a wannan gasa ne ya janyo ba wata Kasa dake mata kallon hadarin kaji duk lokacin da za su gwabza.

A rukunin da Najeriya ke ciki a gasar kasashen nahiyar ta Afrika ta bana sun hada da Kasar Egypt ( Wacce ita ce tafi kowace Kasa samun nasara a wannan gasa ) da Sudan da Guinea-Bissau da kuma Najeriya.

Masu harsahe naganin wannan rukuni  ne mai tsauri. Ko a wanne matsayin Najeriya za ta kare? Lokaci ne zai bayyana.

Jamilu Uba Adamu
Mai Sharhi da bibiyar Tarihin wasan Kwallon K’afa ne.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

An fake da taimako, ana yaɗa da’awar luwaɗi da maɗigo a jihar Kano!

Published

on

 

 

Misbahu Hamza

 

Zuwa Ga Gwamnatin Jihar Kano, Masarautar Kano, Hukumar Hisba, Da Ƙungiyar Mallaman Jihar Kano

Assalamu Alaikum,

Da sunan ƴancin ɗan Adam; da sunan nema wa ƴaƴanmu mata ƴanci da sana’a mai ɗorewa; da sunan taimakawa marayu, gajiyayyu da masu buƙata ta musamman, ana ta ƙoƙarin yaɗa da’awar luwaɗi da maɗigo a jihar Kano!

Ana yaɗa wannan manufa ne a bainar jama’a babu kunya ballantana ganin girmanku ko shakkarku a matsayinku na masu faɗa a ji a jihar Kano—a makarantu da unguwanni. Abin takaici ma har da ma a tsakanin ma’aikatun gwamnati (masu ɗamara)!

Ƙungiyar da ta ke ta wannan mummunan aiki a jiharmu ita ce “Women Initiative for Sustainable Empowerment and Equality.” Suna kiran kansu “WISE” a taƙaice kuma a bayanin da muka gani a shafukan su, har ofishi suke da shi mai zaman kanshi a Yankaba Kawaji, Bompai GRA, Kano.

A wani bayani da muka gani a shafukan wannan ƙungiya, mun ga sun taɓa haɗa bita wa jami’an Hisba, da na KAROTA, da na NDLEA, da sauransu!

Domin tabbatar da duk waɗannan abubuwa, a duba shafinsu kawai na Facebook mai suna “Wise Wage.”

In har wannan ƙungiya ta yi ƙarfin da za ta tara waɗannan jami’ai a wuri guda da sunan yi musu bita—a kan ko ma mene ne—to muna tsoron irin tasirin da suka riga suka yi a cikin jihar mu. Jihar musulunci.

Za ku iya tunawa a makon nan me ƙarewa ne ake ta dambarwar kuɗaɗe da gwamnatin tarayya ta karɓo daga ƙasashen Turai wanda ake zargin cewa ɗaya daga cikin sharuɗɗan amfana da wannan maɗuɗun kuɗaɗe shi ne a sakarwa masu da’awar luwaɗi da maɗigo mara, irin su WISE, su fantama baɗalarsu yadda suke so.

Wannan ya jawo kace nace a ƙasarnan. Kuma mun ga yadda Mallaman jihar Kano ku ka tashi tsaye a mimbari, kamar yadda muka yi tunanin za ku yi, domin yin tofin Allah tsine da wannan yunƙuri matuƙar ya tabbata gaskiya.

Wannan dambarwar ta ƙara bayyanar mana cewa a ƙasarnan akwai doka da kai tsaye ta yi hani da duk wani yunƙuri ko yaɗa manufar luwaɗi da maɗigo. Kuma mun ƙara samun natsuwa ganin yadda Musulmi da Kirista suka haɗa kai domin barranta da wannan ɓarna.

Da wannan muke kiran Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da Sarkin Kano, Mallam Muhammadu Sanusi II, da Shugaban Hisba ta Kano, Mallam Aminu Daurawa, da Shugabancin Kungiyar Mallaman Jihar Kano, da su tabbatar wannan ƙungiya ta WISE ta tattara ƙomatsonta ta bar mana gari kuma a haramta mata aiki a jihar ta kowace hanya da za a iya.

Al’ummar jihar Kano amana ne a wajanku! Kuma Allah zai tambaye ku amanar da ya damƙa muku ranar alkiyama!

Mu mun yi namu—isar muku da saƙon. Idan da ba ku san da wannan kungiya ba ko aiyukanta, to yanzu mun sanar da ku.

Bissalam,

Misbahu Hamza

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Hausa

Wani Attajiri ya ba da kyautar makabarta a garin Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Wani Attajiri Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya ba wa mutanen garin Tsakuwa dake Karamar Hukumar Dawakin Kudu kyautar makabarta.

Shugaban kwamitin Ilimi na Kungiyar Tsakuwa Mu Farka Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ne ya bayyana haka ranar Asabar.

Ya ce attajirin ya danka amanar makabartar ne karkashin kulawar Tsakuwa Mu Farka.

Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ya ce Kungiyar Tsakuwa Mu Farka za ta tattauna yadda za a katange makabartar a taron da shugabannin Kungiyar za su yi nan gaba.

Kunshin sanarwar ya ce “Wannan ita ce tsohuwar Maqabartar Makau wacce dattijon arziki Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya kuma sabunta kyautar ta ga Al’ummar Tsakuwa, karkashin kulawar Kungiyar Tsakuwa Mu Farka. Allahu SWT ya saka masa da mafificin Alkhairi tare da kai ladan gare Shi.

“Idan Allah ya kai Mu taron Shugabancin Tsakuwa Mu Farka da muke gabatarwa online wannan karon zai zo ne a wannan banban dandalin, tattaunawar Meeting din zaifi mai da hankali ne wajen laliban hanyoyin da za mu bi wajen katange wannan makabarta dama sauran makabartunmu da suke garin Tsakuwa.

“Lokaci ya yi da dole sai mun dauko wannan al’adar saboda yadda kullum kasa take kara daraja. Siyan filin makabarta ya fara zamarwa al’umma abu mai wahala birni da kauye.”

Continue Reading

Upcoming Events

There are no upcoming events at this time.

Facebook

Twitter

Trending