KANUN LABARAI
Rashin baiwa kananan hukumomi kudadensu ne ke kawo talauci a kasar nan-Bappa Yola
Nasiru Yusuf
Mai taimakawa shugaban kasa na musamman kan harkokin siyasa Malam Abdurrahman Bappa Yola ya ce rikewa Kananan hukumomi kason da gwamnatin tarayya ke ba su ne ke ruruta wutar talauci a Najeriya.
Kano Focus ta ruwaito Abdurrahman Bappa Yola ya bayyana hakan ne lokacin taron kaddamar da gamayyar wasu kungiyoyi biyar da suka hadu karkashin sabuwar laima da suka kira ‘CoDEN’.
Malam Yola ya ce baya ga talauci, rashin ba wa ‘Kananan Hukumomi’ kudadensu ya haifar da matsalolin tsaro dake samun kasar nan.
“Rashin samun kudin Kananan Hukumomi shi ne ya kai mu yau, wato talauci da yai yawa a Kananan Hukumomi wanda ya haifar da matsaloli da dama musamman harka ta tsaro.
“Wannan rashin ba wa Kananan Hukumomi kudadensu ya jawo matsala ta talauci wadda ta haifar mana da rashin tsaro.
“Wannan yana da muhimmamnci kwarai da gaske, ya zama cewa Kananan Hukumomi suna cin gashin kan su.
“Manufa gwamnoni su dai na tare kudadensu a Jiha, su ba su kudinsu ya tafi kasa ai musu aiki da shi,” a cewar Malam AbdurRahman Yola.
Ya cigaba da cewa kamata ya yi idan gwamnatin tarayya ta turowa Kananan Hukumomi kasonsu na wata-wata, to lallai ne ya je musu.
Mai taimakawa shugaban Kasar ya ce hakan shi ne zai magance zargin da ake yi wa gwamnatocin jihohi da na tarayya na gazawarsu kan yadda abubuwa ba sa tafiya dai-dai.
Malam Abdurrahman Bappa Yola ya bugi kirjin cewa, tun da gwamnatin shugaba Muhammad Buhari ta hau mulki ba wata Jiha da aka rike mata kasonta daga gwamnatin tarayya, don haka bai ga dalilin da jihohi za su cigaba da rikewa kananan Hukumomi kasonsu ba.
Ya ce irin wannan gwamnatin tarayya take so Jihohi su yi wa Kananan Hukumomi don arziki ya yalwata.
Game da me gwamnatin tarayya ke yi na tabbatar da gwamnoni sun bi umarnin da ta bayar na bai wa Kananan Hukumomi kudadensu, Bappa Yola ya ce
“Gwamnatin Tarayya ta yi na ta, a tsari, duk inda Dimokuradiyya take, Kungiyoyi irin CoDEN ne yakamata su dau gabarar tabbatar da gwamnatocin jihohi sun tabbatar wannan tsari ya tabbatar. Shi ya sa ni ma na zo wannan taro.” Ya ce.
A jawabin sa Farfesa Kamilu Fagge na jami’ar Bayero da ke nan Kano ya ce irin wadannan tarurruka kan taimakawa mulkin Dimokuradiyya.
A cewar sa ta hakan za a san mai yake damun mutane, kuma ya za a yi a warware matsalar don cigaban al’umma.
Daya daga cikin wadanda suka samar da gamayyar ta ‘CoDEN’ Malam Abdullahi Sule daga Kungiyar YEDA ya ce manufar gamayyar shi ne samar da ingantacciyyar Dimokuradiyya da za ta amfani kowa da kowa.
Ya ce manufar su shi ne, tabbatar da cewar kudaden Kananan Hukumomi da na Majalisar Jihohi suna isa asusunsu kai tsaye kuma suna kashe kudadensu ba tare da katsalandan din gwamnoni ba.
Malam Abdullahi Sule ya ce Kungiyoyin da suka samar da gamayyar ta ‘CoDEN’ su ne YEDA da CAJA da CDE da OCCEN da Kuma Renaissance Coalition.
Hausa
Mutane 18,000 sun amfana da aikin ido kyauta ta Gidauniyar Mangal a Katsina
Kimanin marasa lafiya masu rauni 18,000 da ke fama da cututtukan ido daban-daban a jihar Katsina sun amfana da ayyukan kulawar ido da tiyata kyauta da Gidauniyar Mangal ta dauki nauyi tun bayan kafuwarta a shekarar 2016.
Wani mamba na kwamitin amintattu (Board of Trustees) na gidauniyar, Malam Hussaini Kabir, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a yayin kaddamar da aikin tiyatar ido na zangon karshe na shekarar 2025 a Cibiyar Ido ta Katsina.
Kabir ya bayyana cewa kimanin mutane 7,000 ne suka amfana a shekarar 2025 kadai, daga sassan jihar Katsina, jihohin makwabta, har ma da wasu yankuna na Jamhuriyar Nijar.

A cewarsa, gidauniyar ta fara tantance wadanda za su amfana kimanin makonni biyu da suka gabata, inda marasa lafiya da dama suka samu magunguna kyauta da tabarau na likita.
Kabir ya kara da cewa wadanda ke bukatar tiyata an dauki nauyin dukkan zaman asibitinsu gaba daya, yana mai cewa kimanin marasa lafiya 2,000 aka tantance a yayin aikin zangon karshe da ake ci gaba da yi.

Ya sake jaddada kudirin gidauniyar na inganta samun kulawar lafiya, yana bayyana shirin a matsayin wani bangare na nauyin alhakin zamantakewar kamfanoni (corporate social responsibility).
“Manufarmu ita ce tallafa wa kokarin gwamnati tare da rage nauyin kudin kula da lafiya ga mafi rauni, musamman wadanda ke fama da matsalar biyan bukatun rayuwa,” in ji shi.

Wani likitan ido a cibiyar, Dokta Ahmad Hamza, ya bayyana cewa an gano marasa lafiya da dama na fama da cutar idon toka (cataract) da glaucoma, cututtuka da galibi ke bukatar tiyata.
Ya jaddada muhimmancin duba ido akai-akai, yana mai cewa gano cuta da wuri na taimakawa wajen hana asarar gani ta dindindin da cututtukan ido masu zuwa a boye ke haifarwa, kamar glaucoma, cataract da lalacewar macula (macular degeneration).

Daya daga cikin wadanda suka amfana, Malam Yusufa Usman, ya ce ya shafe sama da shekaru biyu yana fama da matsalar gani amma ba shi da ikon biyan kudin tiyata.
“Tsawon shekaru biyu ban iya gani sosai ba, amma yau na yi tiyata kuma ina da fatan ganina zai dawo.
Ina rokon Allah Madaukakin Sarki ya saka wa Gidauniyar Mangal da alheri bisa wannan kyakkyawan aiki.
“Ina fatan sauran masu kudi za su yi koyi da wannan abin a yaba,” in ji Usman.

Wata mai amfana, Aisha Muntari daga kauyen Bakuru, ta bayyana kwarewarta yayin da take jiran a kai ta dakin tiyata.
Muntari ta ce ta kamu da matsalar ido kimanin shekara guda da ta wuce kuma ta kusa yanke tsammani kafin ta samu labarin shigar gidauniyar, tana mai bayyana kwarin gwiwar cewa nan ba da dadewa ba ganinta zai dawo.
Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano
Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”
Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye
Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.
Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.
