KANUN LABARAI
‘Yan sanda a Kano sun kama wanda ya kashe abokinsa a kan takalmi

Aminu Abdullahi
Rundunar ‘yan sandan Kano ta kama wani matashi mai suna Nura Sulaiman bisa zargin kashe abokinsa mai suna Abubakar Abdulkarim.
Kano Focus ta ruwaito cewa mai magana da yawun rundunar Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana haka a ranar Litinin.
Ya ce sun samu korafi a ranar biyu ga watan da muke ciki daga unguwar Sauna Kawaji inda wani mutum mai suna Abdulkarim ya ce Nura Sulaiman mai shekaru 17 ya cakawa dansa Abubakar mai shekaru 17 karfe ya yin da suke fada da hakan yayi sanadiyyar mutuwar sa.
Ya kara da cewa bayan samun korafinne suka garzaya da shi zuwa asibitin Muhammadu Sanusi inda likita ya tabbatar da cewa ya mutu.

‘Yan sanda a Kano sun kama wanda ya kashe abokinsa a kan takalmi
‘Yan sanda sun kama masu sanen waya a masallatan juma’a.
Idan malaman Kano suka fahintar dani zan tuba-Abduljabbar Kabara
Ya kuma ce tuni suka kama wanda ake zargin kuma da zarar sun kammala bincike za su mikashi gaban kotu don girbar abinda ya aikata.
A nasa bangaren wanda ake zargi Nura Sulaiman ya ce fada ne ya shiga tsakanin su saboda marigayin yasa masa takalmi.
Ya ce saida mutane suka rabasu yayin da suka kaure da fada, amma suka cigaba da yi inda a nan ne ya caka masa karfe.
Ya kara da cewa bayan da ya caka masa karfe bai yi zaton ya mutu ba domin daya daga cikinsu ne ma ya kai abokin nasu shagon saida magani.
Ya ce da daddare ne mahaifinsa ya fada masa cewa wanda suka yi fada tare har takai ga ya caka masa karfe ya rasu.

Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
