Connect with us

Hausa

Kungiyar Vigilante ta zargi rundunar ‘yan sandan Kano da bata mata suna

Published

on

Aminu Abdullahi

Kungiyar Vigilante a jihar Kano ta zargi rundunar ‘yan sandan jihar Kano  da yinkurin bata mata suna da kuma yi mata sojan gona a ayyukanta.

Shugaban kungiyar Muhammad Kabiru Alhaji ne ya yi wannan zargi a wani martani da ya mayar ranar Alhamis kan wani mai kwacen waya da ake zargin dan kungiyar ne da Rundunar ‘yan sandan ta kama.

Ya ce wanda ake zargin mai suna Walid Abdussalam mai shekaru 19 da aka kama a ranar 4 ga watan da muke ciki ba dan kungiyar su bane.

Ya ce akwai wani dan sanda mai suna Nura Saleh Haske mai mukamin mataimakin sufurtandan ‘yan sanda a Bompai da ya bude ofishin kungiyar a unguwar Sheka Danfodio tare da daukar yara da suke aiki tare.

Ya ce a cikin yaran ne aka kama wanda ake zargi da kwacen wayar kuma ko kadan basu da rijista da uwar kungiyar ta jiha.

‘Yan Sanda a Kano sun kama dan Vigilante na kwacen waya

‘Yan Vigilante sun kubutar da mata 4 da akayi garkuwa da su a Kano

‘Yan sanda sun kama yan fashi uku a Jogana

“Na duba record banga sunan irin wadan nan mutane ba kuma a cikin rijista da ake yi ta kungiyoyi muna da doka ta 5 ta 2012 na duba naga babu wata kungiya da tayi kamanceceniya da inda wadannan yaran ke aiki.

“Akwai wanda yake yin rijista a ofishina, ya bani labari cewa akwai wani dan sanda ana ce masa Nura da ke aiki a bomfai shi yazo yana neman ayi masa rijista ba ai masa ba,” a cewar sa.

Ya ce ya bude ofishin ne ba tare da ambashi rijista ba.

Ya ce a tsarin su ba ‘yan sanda ne ke neman a yi musu rijista su kafa kungiyaba, mutanen unguwa da ke son samar da tsaro a unguwannin su ke neman rijista.

” Dan sandan shi kadai yazo yake so a bude masa kungiya daga karshe da bamu bude ba ya je ya bude ya dibi yara ba tare da sanin mu ba.

“Ya zo ya kai sau uku na ce masa bana yiwa mutum daya rijista, ba mai unguwa da sauran manyan unguwa,” a cewar sa.

Ya kara da cewa idan kungiyar ce ta bada rijista akwai lamba da majalisar dokoki tayi doka da sa hannun shugaba da wakilin ma’aikatar Shari’a.

Sai dai a nata bangaren rundunar ‘yan sandan Kano ta musanta zargin ta bakin mai magana da yawun rundunar Abdullahi Haruna Kiyawa.

Ya ce idan har ana zargin jami’in ‘yan sanda da aikata wani laifi kamata ya yi a sanar da nagaba dashi.

Sai dai ya ce babu wanda ya kaiwa hukumar korafi hasalima ba a tura wani dan sandan ya bude ofishin Vigilante ba.

“Muna aiki da ‘yan Vigilante karkashin tsarin community Police amma babu wanda ya fada mana ko ya rubuta mana cewa dan sanda ya bude ofishin Vigilante,” a cewar sa.

Hausa

Mahaya dawaki sun kashe mutune 2 a Kano

Published

on

Aminu Abdullahi

Wasu magidanta biyu ‘yan gida daya sun rasu sakamakon banke su da mahaya Dawaki su ka yi yayin da suka bisa babur a titin  Sokoto Road da ke Kano.

Kano Focus ta ruwaito cewa ranar Asabar ne mahaya Dawakin suka kashe Inuwa Sani da Abdulrahaman Sani ‘yan unguwar Yakasai a Birnin Kano.

Mahaifiyar su, Rukayya Ali ta ce an kashe ‘ya’yan na ta ne akan hanyar su ta zuwa gaishe ta.

Ta ce kowanne daga cikin marigayan  ya mutu ya bar mata daya  daya ‘yaya shida.

Rundunar ‘yan sandan Kano ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin kakakinta Abdullahi Haruna Kiyawa.

Ya ce suna zargin wani matashi Sadiq Adamu, 22, da abokansa bakwai ne suka shirya hawan Dawakin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutanen.

Ya ce sun kama biyu daga cikin wadanda ake zargi kuma da zarar an kammala bincike za a gurfanar da su gaban kotu.

Masarautar Kano dai ta haramta hawan Dawaki a cikin birinin Kano sakamakon jikkatawa ko hallaka jama’a da mahayan ke yi.

Continue Reading

Hausa

Kishi: Mata a Kano ta hana a yiwa mijinta jana’iza a gidansa

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

Tsananin kishi ya sanya wata mata Jamila Muhammad hana shigar da gawar mijinta cikin gidansa domin yimasa jana’iza bayan rasuwarsa.

KANO FOCUS ta ruwaito al’amarin ya faru ne ranar Litinin a unguwar Gwazaye da ke yankin Dorayi a karamar hukumar Gwale, da ke nan Kano.

Abdullahi Mustapha guda ne daga cikin wadanda suka sheda al’amarin ya shaidawa shirin ‘yan zazu na gidan rediyon Dala cewar tsananin kishi ne ya hana matar amincewa a ajiye shi a gidanta.

Ya ce matar na zaune ne a gidan mijin bayan da kotu ta raba aurensu ta kuma umarceshi da ya bata dama ta ci gaba da zama a gidan saboda yara.

Ya kara da cewa matar ta nemi su rabu da mijin ne don kawai ya auri wata matar.

Sai dai bayan auren sabuwar matar ne kuma auren ya rabu, haka kuma gidan ya koma hannunta.

Mustapha ya ce bacin rai da takaicin matar ne ya haifarwa mijin ciwon zuciya har ya mutu.

Bayan mutuwar tasa ne kuma aka daukoshi daga asibiti aka kuma kaishi gidan da matar take amma fafur ta ce ba za a yi masa sutura a gidan ba.

A cewar Mustapha ba irin bakin da ba a baiwa Jamila ba, amma ta ce sai dai a kaishin gun amarya a yi masa jana’iza.

Hakan ta sanya wani dattijo a unguwar ya bada damar a shigar dashi gidansa domin yi masa jana’iza.

Tuni dai yan uwan Jamila suka dauke ta zuwa garinsu da ke Gezawa domin gudun abinda zai faru.

Continue Reading

Hausa

Hisbah ta nemi taimakon Saudiyya kan dakarunta

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta nemi taimakon kasar Sadiyya da ta tallafa mata wajen horar da jami’anta akan sha’anin aikinsu.

Kano Focus ta ruwaito babban Kwamandan Hisbah, Muhammad Harun Sani Ibn Sina ne ya yi rokon a ofishinsa ranar Lahadi.

Wanan na zuwa ne bayan da hukumar ta karbi bakuncin daya daga cikin limaman Masallacin Harami na Makkah Farfesa Alhassan Bin Abdulhameed Albukhary tare da ayarinsa.

Ayarin Limanin sun ziyarci Kano ne bisa gayyatar Jami’ar Bayero don horarwa ta musamman ga alkalai da daliban ilimi wanda wannan ita ce horarwa irinta ta hudu da suka yi a kasar nan.

Hisbah ta kama matar da ta yi safarar jariri daga Delta zuwa Kano

Ramadan:Hisbah ta kama Gandaye 11 a Kano

Shigar mata: Hisba ta kama wani saurayi da ya rikide zuwa Amina a Kano

“Babban kalubalenmu shi ne rashin wurin da za mu horar da jami’anmu domin su kara samun horo a kan ayyukansu.

“Zai yi kyau idan har za mu samu tallafi daga Hukumar Kasar Saudiyya mai albarka wajen samar mana da wuri ko kuma makarantun da jami’anmu za su dinga samun horo ko da kuwa a kasar Saudiyya din ne.” cewar Ibn Sina

A nasa Jawabin Imam Albukhariy ya yaba wa hukumar Hisbah akan ayyukan da take gudanarwa a fadin jihar nan, inda ya nemi su rubanya kokarinsu akan ayyukansu.

“Shi aikin umarni da aikin alheri da hani da mummuna abu ne babba a harkar zamantakewar al’umma.

“Wasu malamai suna cewa da za a kara wani abu a kan rukunan Musulunci to da abin da za a kara ba zai wuce umarni da aikin alheri da hani da mummuna ba saboda muhimmancinsa a Musulunci.

“Don haka ’yan Hisbah ku sani aikin Allah kuke yi.”

Farfesa Albukhari wanda shi ne Shugaban Sashen Larabci na Jami’ar UmmulQura da ke garin Makkah ya bayyana cewa, Hukumar Kasar Saudiyya za ta taimakawa hukumar Hisbah da duk irin abin da take bukata, matukar dai bai ci karo da tsarin mulkin kasar ta Saudiyya ba.

Continue Reading

Trending