KANUN LABARAI
Rundunar ‘yan sandan Kano ta kama wani ‘boka’ da ke shirin kwakule idanun jariri
Mukhtar Yahya Usman
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wani mutum mai suna Yahya Shehu da ake zargin ‘bokane’ da ya nemi kwakule idon jariri domin hada layar zana.
Kano Focus ta ruwaito kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya yi holinsa a shalkwatar rundunar a ranar Litinin.
Kiyawa mai mukamin mataimakin sufurtandan ‘yan sanda ya ce sun kamo bokanne bayan da wani matashi mai suna Kabiru Sani ya shigar da korafi gaban ‘yan sanda.

Ya ce ba su yi wata-wata ba suka mamaye shi suka kuma damke shi.
Kiyawa ya ce sun samu kayan tsafi a tare da shi da suka hadar da layu da kyallen likkafani dawata kasa, sai kwarya da aka yi mata rubutun ‘dalasimai a ciki.
Da ya ke bada bayanin yadda al’amarin ya faru matashi Kabiru Sani ya ce ya je gurin bokan ne domin neman maganin rashin lafiyar da ke damun sa.
A cewarsa ya bashi magani da wani ruwa ya ce ya gauraya da fitsarinsa har tsahon kwana uku.
“Naje gurin Malam Yahya saboda bani da lafiya sai ya bani magani da wani ruwa ya ce na hada da fitsari na na kuma dawo bayan kwana uku.
“Na dawo bayan kwana uku sai ya kuma bani wani rubutu ya ce naje na yi amfani da shi.
“Ina yin amfani da shi ne kuma sai kaina ya juye daga nan duk abinda ya ce na yi sai na yi masa.
“Haka ya yi ta yi min romon baka da kudi, zai bani miliya daya miliyan biyu.
“Kwatsam sai rannan ya ce naje na kawo jariri za a cire idonsa za a yiwa soja aiki, za a yi masa layar zana.
“Da na tafi sai jikina ya yi sanyi na je na gayawa yayata halin da ake ciki shi ne fa hankalin ta ya tashi.
“Saura kiris mu dauko yaron dan gidan Samira yayata uwarmu daya ubanmu daya amma Allah ya kwacemu shi ne muka kai kara ofishin yan sanda.
Mista Kiywa ya ce a yanzu haka rundunar yan sanda ta fara bincike kuma da zarar ta kammala za ta gurfanar da shi gaba kuliya domin ya girbi abinda ya shuka.

Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
