Connect with us

KANUN LABARAI

Ayi muku kayan daki, ayi muku gara, kuce a soke lefe-martanin ‘yan mata ga samarin Kano

Published

on

Aminu Abdulahi

‘Yan mata da dama ne suka soki kiran shehin malamin nan na Kano Sheik bn Usman na cewar lokaci ya yi da yakamata a soke lefe.

Ya yin zantawar Kano Focus da wasu ‘yan mata a Kano sun nuna rashin amincewarsu karara da wancan kira na malamin, ko da dai wasu sun ce maganar malamin akwai kanshin gaskiya.

Sun ce mlamai basa kulawa da bukatun bagaren mata, ko da yaushe sun fi kula da al’amuran da suka shafi maza.

Suka kara da cewa ana yiwa maza kayan daki a kuma yi musu gara idan za su auri mace, amma ba wanda ya ke cewa a soke wadannan sai dai  a soke lefe.

Idan za a iya tunawa dai a rana juma’ar da ta gabata yayin tafsirin alqur’anin  da yake gabatarwa a masallacin Sahaba deke kundila sheikh bn Usman ya ce lokaci ya yi da yakamata a soke lefe.

Malamin ya ce al’adar yin lefe ta zamewa samarin da ke da niyyar yin aure kadangaren bakin tulu, biyo bayan tsarebe-tsaraben da ke cikinsa.

Ya ce ba yana inkarin al’ada bane sai dai kar al’ada ta shigo da wahalarwa.

Ya kara da cewa al’ada na saka mutane shiga cikin damuwar da ta ke sanyasu siyar da kadarorinsu.

Kiran ya sosa zucuyar ‘yan mata

Sai dai wannan kira da jan hankali bai yiwa ‘yan mata da dama dadi ba, inda galibinsu suke ganin kamar malamin na son jawo musu jangwamne.

Haka zalika wasu ‘yan matan sun yiwa zance malamin karatu na tsanaki inda suka ce akwai kanshin gaskiya a bukatar da ya bijiro da ita.

Mata za su iya tafiya tsirara

Suwaiba Isma’il Gadon Kaya cewa tayi a wannan zamanin da wasu mazan ke da rashin kulawa ga matayensu idan aka soke lefe sai wata matar ta tafi tsirara.

Ta ce wani namijin idan yayi lefe yana shekara biyar bai dinkawa matarsa koda dankwali ba.

“Abin takaici sai namiji ya dinga bin matan waje wai saboda su fes suke, shima tasa ta gidan da zai bata kulawa fes zai ganta.

“Kullunm magana daya malamanmu suke, shi ne marwa jinsin maza sauki amma basa nemawa jinsin mata sauki a aure.

“Mai yasa basa kira ga iyayen yarinya da su dena kayan ɗaki, mazan su dingayi, meyasa basa kira da adena yiwa maza gara su mazan su tanadi kayan abincin.

Maza na anfanuwa da lefe

Ta kuma ce lefen ba iya mata yake taimakawaba har da maza domin ba gidansu matan suke kaiwa ba.

“Wasu abubuwan ma aciki tare zakuyi amfani dasu, kamar mayuka da turaruka.

“Su kuwa iyayenta gara suke daukowa daga gidansu su kawo maka gidan ka,” a cewar Suwaiba.

Khadija Abba Garba dake unguwar Sheka ‘Yar Kasuwa ta ce soke laifen zai sa maza suki daukar aure da mahimmanci.

Rashin lefe zai haifar da sakin mata cikin sauki

Khadija ta kara da cewa lefene ke kara armashin aure, in kuwa har akayi aure ba tare da lefe ba maza za su cigaba da sakin matansu cikin sauki.

Haka kuma zai basu damar yin auri-saki saboda ba za su sha wahalar lefe.

“Za kaga yanxu koda wasu sunaso su saki matansu, zakaji suna cewa yanxu in zan kara aure sai na kuma yin wahalar lefe.

“Ni a ganina wannan batun nasa baiyi ba saboda maza za su dau mata a arha”

“Amma kuma rashin yin lefen shi zai sa maza su ringa yin aure da wuri, sai dai ba zai dinga yin karkoba, kuma ma idan maza sunyi lefen ai su a kewa ado da kayan,” a cewar ta.

Soke lefe zai kawo raguwar zinace-zinace

Binta Garba Makwarari ta ce lefe ya zama tashin hankalin aure a yanzu musamman ma idan wanda zai yi aure bashida hanyoyin samun kudi yadda yakamata.

Ta ce baiwa maza sauki wajen yin aure zai kawo raguwar zinace-zinace da doguwar soyayya.

“Wallahi da za a hakura da lefe da anji dadi a harkar aure.

“Zinace-zinace da doguwar soyayya kafin aure da duk sun yi karanci.

“Sannan duk kokarin da gidan angwaye za su yi su kai wannan lefen idan ba a yi da gaske ba sai an kushe.

“Ya ilahi ina zamu kai dogon buri a rayuwa.” A cewar ta.

 

Ta kara da cewa sadaki kwakkwara yafi lefe tana mai cewa kamata yayi a dinga duba aure a matsayin ibada fiye da nishadi.

Hadiza Yusuf ta ce inda za a bar yin lefe sai anfi zama lafiya tsakanin ma’aurata.

Ta ce dayawan dangin amarya kan zuba ido don ganin lefen da za a kawowa ‘yar su wanda idan bai yi musu ba sai su raina.

“Haka dangin ango dashi kansa angon kan zuba idon ganin me aka zuba adaki, idan baiyiba suma su raina, har ana zuba idon ganin alakoron gara daza a lodo itama rainawa ake daga nan ake fara samun rashin zama lafiya da gori,” inji Hadiza.

Yin lefe ke sa maza rike matansu.

Umar Abubakar wani matashi a nan Kano ya ce baya goyan bayan soke lefe dan kuwa da yawan maza sunfi rike matansu ne la’akari da kudaden da suka kashe yayin auren.

Ya ce idan har aka soke lefe to maza za su cigaba da yiwa aure rukon sakainar kashi, da haka zai sa a cigaba da samun mutuwar aure a kasar hausa.

“Duk abinda aka fada hakane amma maganar gaskiya wasu mazan na yanzu mafi yawansu basa mutunta aurensu.

“Sai namiji ya kashe makudan kudi ya narka lefe nagani na fada amma daga anyi auren sai ya dinga wulankanta matar to yayi lefen kenanfa ina kuma ga baiyi ba.

“Gani zaiyi sadaka aka bashi yana da damar da zai wulakanta yar mutane aganin sa,” a cewar sa.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Trending