KANUN LABARAI
An kama kwarton da ke neman a biyashi kudin yin kwartanci a Kano
Amiunu Abdullahi
Jami’an vigilante sun kama wani kwarto mai suna Abubakar Sadiq da ya kware wajen hada Lamba tare da kiran matan aure domin yin kwartanci da su kuma ya nemi su biyashi lada.
Kano Focus ta ruwaito cewa matashin ya shiga hannun jami’an vigilante din ne a ranar Litinin a unguwar Dorayi da ke birinin Kano, bayan da wata matar aure da ya nema ta yi masa kofar rago.
Shi dai wannan kwarto da aka fi kira da Shanawa mazaunin Unguwa Uku, yana neman matan aure ne kuma ya nemi su biyashi kudin zuwan da ya yi musu.
A cewar jami’an Vigilante Sadiq Shanawa na hada lamba ne ya kuma kira matar da ya samu a layi ya kuma nemi yin lalata da ita.

Sai dai acewar matar da ta yi masa Kofar rago da ta nemi a sakaye sunanta ya kiratane da safe, ya kuma dinga furta mata kalaman batsa lamarin da yasa ta kashe wayar.
Ta ce ya kara kiranta da karfe sha biyu na dare duk da ta fada masa cewa ita matar aurece, amma bai fasaba, sai ma sakonnin batsa da ya dinga tura mata da hakan yasa ta sanar da mijinta abinda ke faruwa.
Ta kara da cewa bayan da ta fadawa mijinta abinda ya faru ne sai ya bata dama data fada masa cewa yazo su hadun.
“Bayan damar da mijina ya bani, shi ne muka sanarwa ‘yan sintiri dake nan unguwar Dorayi.
“Bayan na ce masa yazo, da yazo na hangoshi naga yana kokarin kiran waya sai naga ya saki murmushi nima sai nayi masa.
“Sai nace masa muje shagon cirar kudi dan nacire mana kudin da zamuyi amfani da shi kamar yadda ya nema.
“Domin yaron yace sai na bashi kudi idan har unguwata zaizo.
“Dubu goma zan bashi yace wai wuni zai yi dani hatta kudin a dai-daita sahu ma haka yace ni zan biya masa.
A nasa bangaren Abubakar Sadiq Shanawa yace yana zaune a dakin sa ne sai ya hada number ya kira ta.
Ya kara da cewa bayan ya kira ta sai ya tura mata sako inda ya bayyana mata cewa yana so su hadu su dan huta tare da shakatawa.
“Da ta fadamin haka nayi zaton dawasa take yi ba matar aure bace, don tacemin ita ba halinta bane kuma ba za ta iya aikata hakan ba amma na cigaba da kiranta,” a cewar sa.
A nasa bangaren shugaban gamayyar kungiyoyin kare hakkin dan adam a jihar Kano Karibu Yahya Lawan Kabara yace za su bibiyi lamarin tare da tabbatar da cewa an hukunta wanda ake zargin.
Haka zalika kwamandan ‘yan Sintiri na jihar Kano Muhammad Kabir Alhaji ya tabbatar da faruwar lamarin.
Inda yace tuni suka mika wanda ake zargin ga hukumar ‘yan sanda don girbar abinda ya shuka.

Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
