Connect with us

KANUN LABARAI

‘Yan Vigilante sun kama wanda ke labewa a kwana yana kama ‘yan mata

Published

on

Aminu Abdullahi

Jami’an Vigilante sun kama wani magidanci mai suna Ibrahim da ke zaune a unguwar yan awaki a karamar hukumar Tarauni, bisa zargin labewa a kwana yana cakumar \yan mata, da matan aure.

Kano Focus ta ruwaito cewa an kama wanda ake zarginne mai ranar Litinin bayan daya dakumi mazaunan wata matar aure, lokacin da ta ke tsaka da tafiya.

Matar auren da ta nemi a sakaye sunanta ta ce tana cikin tafiya kawai sai wanda ake zargin ya biyo ta bayanta a dakume mata mazaunai. A cewarta ta yi tunani zai kauce ne ya bata hanya ko kuma ita ta kauce masa amma sai kawai taji ya aikata wannan barna.

“Ji nayi kawai an rikemin mazaunai, sai ya wuce da ya yi gaba sai yaga maza ya yi tunanin zanyi masa ihu sai ya dawo sai nace masa Allah ya yarda sai anyiwa ‘ya’yan shi shine ya ce nayi hakuri.

“Ashe yana biye dani dazan dawo ma sai  na sake ganin sa har ya canza hanya sai ya sake biyowa inda nake shi ne nace masa sake yimin zakayi to wallahi ka tabani kagani shi ne ya wuce baice komai ba,” a cewar ta.

Jami’an Vigilante a Kano sun kama barawon baburin Opay na zuwa burge ‘yan mata

‘Yan Vigilante sun kama dilan kwaya a kasuwar ‘yan Kaba

‘Yan daba sun kone gida jami’in Vigilante tare sassara kwamadansu a Kano

Itama wata matar aure ta ce wanda ake zargin yana sanya takunkumin rufe fuska don kada a gane shi, wasu lokutanma sai a yi zaton wani yake jira.

Ta kara da cewa ya dauki lokaci mai tsayi yana yiwa matan dake wucewa barazana musammanma idan rana tayi yayin da mazajen yankin suka fita neman abinci.

A nasa bangaren wanda ake zargin Ibrahim Isma’il mazaunin unguwar Hotoro Tsamiyar Boka ya ce a kalla ya kaiwa mata guda biyar hari.

A cewarsa ya shafe watanni biyu yana aikata muguwar ta’adar tasa, ya kara da cewa duk da yana da aure amma karfin sha’awane yasa shi aikata haka.

Kwamandan ‘yan Vigilante dake ‘Yan awaki mai suna Adamu Abubakar Fiya-fiya ya ce sun shafe watanni uku suna farautar wanda ake zargin,

Amma sai a wanna lokaci Allah ya basu damar kamashi.

Ya ce akwai matan da suka kawo musu korafin cewa yana taresu tsakanin bayan masallacin juma’a na ‘Yan awaki zuwa wani layi dake bayan wata makaranta mai zaman kanta a unguwar.

“Mun kamashi kuma zamu mika shi hannun hukumar Hisbah don girbar abinda ya aikata,” a cewar sa.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Hausa

Wani Attajiri ya ba da kyautar makabarta a garin Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Wani Attajiri Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya ba wa mutanen garin Tsakuwa dake Karamar Hukumar Dawakin Kudu kyautar makabarta.

Shugaban kwamitin Ilimi na Kungiyar Tsakuwa Mu Farka Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ne ya bayyana haka ranar Asabar.

Ya ce attajirin ya danka amanar makabartar ne karkashin kulawar Tsakuwa Mu Farka.

Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ya ce Kungiyar Tsakuwa Mu Farka za ta tattauna yadda za a katange makabartar a taron da shugabannin Kungiyar za su yi nan gaba.

Kunshin sanarwar ya ce “Wannan ita ce tsohuwar Maqabartar Makau wacce dattijon arziki Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya kuma sabunta kyautar ta ga Al’ummar Tsakuwa, karkashin kulawar Kungiyar Tsakuwa Mu Farka. Allahu SWT ya saka masa da mafificin Alkhairi tare da kai ladan gare Shi.

“Idan Allah ya kai Mu taron Shugabancin Tsakuwa Mu Farka da muke gabatarwa online wannan karon zai zo ne a wannan banban dandalin, tattaunawar Meeting din zaifi mai da hankali ne wajen laliban hanyoyin da za mu bi wajen katange wannan makabarta dama sauran makabartunmu da suke garin Tsakuwa.

“Lokaci ya yi da dole sai mun dauko wannan al’adar saboda yadda kullum kasa take kara daraja. Siyan filin makabarta ya fara zamarwa al’umma abu mai wahala birni da kauye.”

Continue Reading

Hausa

Ba bu inda nace nafi Yan Najeriya shan wahalar Tsadar rayuwa, amma ina Fatan matsalar ta zamo tarihi -Dangote

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

Shugaban rikunin kamfanonin Dangote Alhaji Aliko Dangote ya nisanta kansa da wani labari da ake yadawa a kafafen sada zumunta na zamani cewa yafi yan Najeriya shan wahalar tsadar rayuwa.

Dangote ya tabbatarwa da yan kasa cewa, wasu ne suka dauki nauyin yada labarin domin bata masa suna a daidai lokacin da Yan Najeriya ke cikin halin ‘kaka na kayi’ saboda wahalhalun da ake fama da su .

Sanarwar ta nemi Yan kasar nan da suyi watsi da labarin, inda Dangote yayi fatan kawo karshen matsalar da ake ciki a Najeriya.

“Duk abinda ya shafi yan Najeriya ya shafemu”, inji Sanarwar.

Dangote ya Kara dacewa, ”an kawo maganar faduwar darajar Naira da sayan kaya da Dala ne domin cimma wasu bukatu na kashin Kai bukatun  da basu samu damar biya ba a baya.”

Kamfanin na Dangote na sarrafa siminti da takin zamani da kuma tatar man fetur. A  bangaren kayan abinci kuma, Kamfanin na sarrafa sikari,  gishiri da kayan dandanon girki ne kadai.

“Muma muna siyan muhimman kayan abinchi a kasuwa kamar yarda kowa ke siya don amfanin kanmu da kuma bayarwa wajen  ciyar da al’umma.” Dangote.

 

Shugaban kamfanin yayi mamakin yadda ake neman haddasa sabani tsakanin Kamfanonin Dangote da bangaren gwamnatin tarayya, inda yace shi dan kasuwa ne ba dan siyasa ba, don haka babu inda yayi maganar kalubalantar Gwamnatin tarayya.

“Kamfaninmu ya kasance me bin dokokin kasa a koda yaushe tare da  neman sauki ga al’umma da fatan alheri.”

Saboda haka, sanarwar ta nemi Yan Nigeria su guji daudar sakon da yake ba daga kamfani yake kai tsaye ba, tare da yada  rade-radi da jita-jita.

Continue Reading

Upcoming Events

There are no upcoming events at this time.

Facebook

Twitter

Trending