Connect with us

Hausa

Matsin rayuwa: Matashi a Kano ya saci injin masallaci domin yin kayan sallah

Published

on

Aminu Abdullahi

Jami’an Vigilante da ke Unguwar Hotoro sun kama wani matashi mai suna Dayyabu Inuwa da ya saci injin masallacin domin ya siyar ya yi dinkin sallah.

Kano Focus ta ruwaito matashin ya shiga hannu ne bayan da wani jami’in Vigilante ya yi masa Kofar rago  ya sace a Unguwa Uku da ke karanar hukumar Tarauni ranar Talata.

A cewar kwamandan vigilante na Hotoro Adamu Abubakar daya daga cikin ma’aikatan su ne ya kama wanda ake zargin ya yin da yake kokarin guduwa a kan babur.

Ya ce bayan hongo wanda ake zarigin ne ya nemi taimakon al’umma aka yi tara-tara aka kamashi.

Bayan sun kaishi ofishin su ne kuma ya tabbatar musu da sato injin ya yi a wani masallaci khamsu salawati a Unguwa Uku.

Ya kuma ce da zarar sun kammala bincike za su mikashi ofishin ‘yan sanda don daukar mataki na gaba.

‘Yan Vigilante sun kubutar da mata 4 da akayi garkuwa da su a Kano

‘Yan Vigilante sun kama wanda ke labewa a kwana yana kama ‘yan mata

‘Yan bindiga sun kashe dan vigilante suka yi garkuwa da wata mata a garin Falgore

Da yake amsa tambayoyin hukuma, wanda ake zargin ya ce ya saci injin ne domin ya siyar ya yi siyayyar sallah.

Ya kara da cewa yana shan tabar wiwi da kwaya da hakanne yasa ya aikata hakan.

Ya kara da cewa wannan ne karon farko da ya tabayin sata a  masallaci a watan azumi.

A nasa bangaren ladanin masallacin Ustaz Yunusa Kalla ya ce masallacin ya dade babu inji har sai da wata baiwar Allah ta siyawa masallacin.

Ya kara da cewa akwai yara da suke yin karatun Islamiyya da asubah da hakanne yasa aka bar masallacin a bude.

“Yayi amfani da wannan damar ne wajen shiga ciki, sai dai Alhamdullillah an kamashi tare da inji tun kafin yaje ya siyar,” a cewar sa.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Yunkurin tsige Malam Ibrahim Khalil wasan yara ne – Prof. Alkafawy

Published

on

Malam Ibrahim Khalil

Nasiru Yusuf

Majalisar Malamai ta Kasa ta bayyana yunkurin tsige Malam Ibrahim Khalil daga shugabancin Majalisar Malamai ta Jihar Kano da cewa wasan yara ne.

A wata sanarwa da KANO FOCUS ta samu Mai dauke da SA hannun Sakataren Kungiyar Farfesa Muhammad Sadik Alkafawy ya sanyawa hannu ranar Alhamis ta ce abun da aka yi ba ya bisa doka.

Ga cikakkiyar sanarwar:

“Majalisar  Malamai ta Kasa ta sami labarin yunkurin wata jama’a da ke kiran kanta Malamai, amma ta bari wasu wadanda ba su nufin alheri su yi amfani da su a kawo baraka tsakanin jama’ar Musulmi. Wannan abin takaici ne.

“Tun daga ranar da a ka assasa Majalisa zuwa yau ba a taba samun tabargaza irin wannan ba. Don haka Majalisa ta Kasa na yin kira ga wadannan mutane su tsoraci Allah su kauce ma son zuciya.

“Hakika Majalisar Malamai reshen jihar Kano ta yi daidai da tace wadanda su ka shiga wannan bankaura ba ‘ya’yanta ba ne tun daga jiha balle na Kasa. Yaya za a yi wanda ba ya cikin Majalisa ya ce ya kori wanda a ka kafa Majalisa da shi?.

“A wurin Majalisa ta Kasa abinda a ka yi ba ya bisa doka, kuma wasan yara ne. Hasali ma fata mu ke Allah ya ba shi shugabancinta na Kasa baki daya, amin.

“A karshe, Majalisar kasa ta yi mawafaka da duk abinda Majalisar Kano ta tsaya a Kai. Alhamdu Lillah.”

Continue Reading

Hausa

Tijjanawa ba sa goyon bayan nadin Pakistan shugaban Majalisar Malamai – Alkarmawi

Published

on

Khalifa Abdulmajid Alkarmawi

Khalifa Abdulmajid Alkarmawi

 

 

 

 

بسم الله الرحمن الرحيم 

وصلي الله علي النبي الكريم 

Majalisar Malamai ta jihar Kano tana da mahimmanci ga Musulmin Arewacin Nigeria gaba daya ba Kano ba kawai, don ko ba komai Al’ummar Musulmi suna kara samun hadin kai da magana da murya daya sanadiyar wannan majalisar kuma babban abun bukata shine hadin kan Musulmi.

Amma sabon shugabanci da akai jiya (Litinin) da aka nada Malam Abdallah Saleh Pakistan (Shugaban Izala na jahar kano) zai iya rusa majalisar ma gaba daya, Saboda Shugabancin yana bukatar malamin da yake Zaune lafiya da duk akidun Musulunci da suke Kano, wanda Pakistan kuwa yana da matsala da wasu bangarorin.

Shawarata kowa a nan shine Asami malamin da yaki da kyakkywar alaka da kowa ya jagoranci Alumma Sai asami kai wa ga gaci.

Don haka a madadin Tijjanawa, gaskiya gabadayanmu musamman na jihar Kano muna sanar da cewa ba ma tare da Shugabacin Malam Abdallah Saleh Pakistan.

Khalifa Abdulmajid Alkarmawi

Shugaban Khuddamur Rasul SAW na Afrika

Continue Reading

Hausa

Gamayyar Malaman Kano sun nesanta kan su daga tsige Malam Ibrahim Khalil

Published

on

Sheikh Ibrahim Khalil

Nasiru Yusuf

Gamayyar Malaman Jihar Kano da suka kunshi jagororin darikun Tijjaniyya da Qadiriyya da kuma Salafiyya sun yi watsi da sanarwar tsige Malam Ibrahim Khalil daga shugabancin majalisar malamai.

Wata sanarwa da KANO FOCUS ta ci karo da ita dauke da sa hannun sakataren gamayyar Malaman, Dr Sa’idu Ahmad Dukawa ranar Talata malaman sun ce ba da yawunsu aka dauki wannan mataki ba, kuma ba sa goyon bayansa.

Malaman da suka sahale a fitar da sanarwar sun hada da Shugaban Darikar Kadiriyya na Afrika ta Yamma Sheikh Karibullahi Sheikh Nasiru Kabara da Sheikh Abdulwahab Abdallah da Sheikh Ibrahim Sheh Maihula da Dr. Bashir Aliyu Umar da kuma Imam Nasir Muhammad Adam ( Shugaban majalisar Limaman masallatan Juma’a).

Sauran sun hada da Farfesa Musa Muhammad Borodo da Farfesa Muhammad Babangida da kuma Dr. Ibrahim Mu’azzam Maibushira.

Continue Reading

Trending