KANUN LABARAI
KANSIEC na neman cinye mana hakkokinmu-jami’an zaben kananan hukumomi
Aminu Abdullahi
Makwani uku da gudanar da zabukan kananan hukumomi a jihar Kano amma har yanzu ba a biya wadanda suka gudanar da aikin zaben hakkinsu ba.
A zantawa ta musamman da jaridar Kano Focus wasu daga cikin wadanda suka gudanar da aikin sunce har yanzu hukumar bata waiwayesu ba kan batun biyansu hakkokin nasu.
Balaraba Musa na daga cikin wadada suka gudanar da aikin zaben yace hukumar ta ce za ta biya su hakkokinsu kwanaki biyu bayan kammla zaben ne, sai dai har yanzu shiru kake ji.
“Nayi aiki ne a mazabar Zaitawa dake Karamar Hukumar Birni, a kwati mai lamba 014.

“Ina kira ga gwamnati da ta taimaka ta biyamu hakkokin mu,” a cewar ta.
Itama Zainab Ibrahim ta ce duk da cewa ta fito a kan lokaci zuwa inda aka turata amma har yanzu shiru take ji malam yaci shirwa.
“Nayi aikina ne a mazabar Shahuci da ke Karamar Hukumar Birnin
“Sanda zamuyi aikin sunce za su tura mana da kudaden mu asusun banki,” a cewar ta.
Haka kuma Abdulsalam Abubakar da ya yi aikin zabe a mazabar Tukuntawa ya ce a ka’ida sati daya da yin zabe za a biyasu hakkokin su, amma har an shiga sati na uku ba tare da jin wani labariba.
“Wasunmu dalibaine, gashi yanzu an koma makaranta amma ba a biya mu ba,” inji shi.
Kudinmu za su iya salwanta
Isah Abdullahi da ya yi aikin zabe a Mazugal dake karamar hukumar Dala ya ce yana tsaron kada hukumar zabe ta hanasu hakkokinsu baki daya.
Ya kara da cewa bai kamata a ce hukumar zaben tayi jinkirin biyan su hakkokinsu ba duba da cewa sun fita guraren da aka tura su akan lokaci kamar yadda aka umarce su.
Ya kuma ce sun bi dukkan matakan da suka da ce don ganin an biyasu hakkokinsu, sai dai har yanzu shiru suke ji.
“Indai muka je sai suce mukara hakuri zamu ji alart, gaskiya muna fargabar kada su cinye mana kudaden mu, ” a cewar sa.
Ba ma so a sake cinyewa wasu kudi ne
Sai dai hukumar zabe ta jihar Kano KANSIEC ta matsalar da aka samu ayin zaben da aka gudanar a baya ce ta sanya jinkirin.
Mai magana da yawun hukumar Dahiru Lawan Kofar Wambai ya ce a shekara 2018 an samu matsaloli na son zuciya daga gurin turawa zaben kananan hukumomi.
Ya ce a wancan lokacin turawan zabe aka baiwa kudaden ma’aikatan wucin gadi a hannu, don su biya su amma a karshe da yawan wadanda suka yi aikin ba a biya su hakkokinsu ba.
Ya kara da cewa hakan tasa a wannan karon hukumar zabe tayi tsari, ta yadda duk wanda ya yi aiki zai samu hakkinsa ba tare da an rage masa wani abu ba.
“A yanzu muna kan tantance lambobin asusun bankin wadanda suka yi aikin ne don gudun kada a samu matsala.
“kowa za a biya shi hakkinsane ta lambar asusun bankin da ya bayar nan bada jimawa ba,” a cewar sa.
Sai dai a duk bayanin da yayi bai bayyana lokacin da za su biya ma’aikatan ba.
Idan za a iya tunawa dai ko a shekarar 2018 akwai ma’aikatan wucin gadin da suka gaza samun hakkokinsu na ayyukan zabe da suka yi.
Wadanda kuma har yau dinnan ba su samu ba, hakan ta sanyan galibinsu ke tsoron kar a cinyemsu.

Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
