Connect with us

Hausa

An bude kamfanin leken asirin masoya da ma’aurata a Kano

Published

on

Aminu Abdullahi

Wani matashi, Sulaiman Muhammad ya bude kamfanin leken asirin masoya da ma’aurata a Kano.

Kano Focus ta ruwaito matashin wanda dalibi ne a jami’ar Bayero da ke nan Kano ya kirkiro sana’ar ne domin yiwa ‘yan mata ko matan auren leken asirin abinda mazajesu ko matayensu ke aikatawa a lokacin da basa tare.

Ya ce mace za ta iya basu kwangilar bibiyar inda mijinta ko saurayinta ke zuwa, don sanin ko yana yi mata karya.

Haka zalika ya ce idan har miji ya cewa matar sa ya tafi gurin aiki to su kuma za su bibiya su gano gurin aikin ya tafi ko wani gurin na daban.

A cewarsa duk wanda ya ke so a yi masa irin wannan leken asiri to zai biya kudi a mataki uku.

Matakin farko za a biya N10,000 domin sa ido jigari-jigari, sai kuma mataki na biyu da za a biya N15, 000 domin tsanantawa ba kamar na baya ba.

Haka zalika mataki na uku wanda shi ne babban za a biya N25,000 domin binciken kwakwkwafi da kuma bin diddigin halin wanda ake bukata ke ciki.

Sana’a ko munafurci

To sai dai bullar wannan sabuwar sana’a ce  samari da ‘yan mata a Kano suka  bayyana ra’ayoyinsu, inda wasunsu ke kallonta a matsayin munafurci zalla.

Aisha Taiyo Ibrahim mai shekaru 23 da ke zaune a unguwar Hotoro ta ce sana’ar leken asiri ta saba ka’ida.

A cewarta idan duk abinda mutum ya yi za a dinga bibiyar sa to hakan zai haddasa zargi da rashin fahimta a tsakanin masoya.

Bakin talauci yasa an bude tashar ‘Buhari’ a Kano

Gwamnatin tarayya ta amince a bude sabbin jami’o’i uku a Kano

Kungiyar ‘yan gwanjo ta gudanar da adduo’in neman zaman lafiya a Kano

Ta kara da cewa bai kamata a ce mace ta sa ana bibiyar inda saurayin ta ko mijinta yake zuwa ba.

” Yanzu ka sanar da ita zaka je gurin aiki sai a gurin aikin akace ka biya ta wani gurin.

“To su inda suka ga ka tsaya nan za su fada mata tunda ba za su san dalilin da ya tsaida kai ba.

“Daga nan kuma zargi zai shiga sai alaka ta lalace gaskiya ni bana goyan baya, domin a addinance da kundin tsarin mulki duk sun haramta haka,” a cewar ta.

Rukayya Adam mai shekaru 24 daliba a jami’ar Yusuf Maitama Sule ta ce bata goyan bayan yin leken asiri ga miji ko saurayi.

“Kazantar da baka gani ba ai tsafta ce, shi namiji yana da hanyoyi kala-kala,, gwanda dai kowa yaji tsoron Allah kawai.

“Kuma su masu irin wannan sana’ar za su iya bada abinda ba gaskiya bane akan mutum, kaga daga nan sai zargi ya shiga ciki,” a cewar ta.

Habiba Abu Haruna mai shekaru 24 da ke unguwar Jambulo cewa tayi rashin basira ne mace tasa ana bibiyar mijinta domin wataran za ta tono abinda bata sani ba.

Ta kara da cewa gwara a cigaba da tafiya a haka don gudun kada a tono abinda ba zai yiwa kowa dadi ba.

“Koda zai yi  karya, kansa yayiwa, yanzu kaduba yadda mata ke kashe mazajen su ta hanyar yin bincike a waya, ina kuma a ce sawa suke ana bibiyar sa kaga abin sai yafi haka,” inji ta.

Mika’il Yunus wani magidanci da ke unguwar Hausawa mai shekaru a shirin da bakwai ya ce ko kadan ba zai iya sawa a dinga bibiyar abokiyar zaman sa ba.

“Wannan ai ba sana’a bace munafurcine don ko turawa basa yin haka balle mu hausawa kuma musulmai.

“Ni ina ganin kamata ya yi su canza sana’a amma ba wannan ba, don wannan ba abinda za ta kara sai rigingimu a tsakanin masoya,” a cewar sa.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Yunkurin tsige Malam Ibrahim Khalil wasan yara ne – Prof. Alkafawy

Published

on

Malam Ibrahim Khalil

Nasiru Yusuf

Majalisar Malamai ta Kasa ta bayyana yunkurin tsige Malam Ibrahim Khalil daga shugabancin Majalisar Malamai ta Jihar Kano da cewa wasan yara ne.

A wata sanarwa da KANO FOCUS ta samu Mai dauke da SA hannun Sakataren Kungiyar Farfesa Muhammad Sadik Alkafawy ya sanyawa hannu ranar Alhamis ta ce abun da aka yi ba ya bisa doka.

Ga cikakkiyar sanarwar:

“Majalisar  Malamai ta Kasa ta sami labarin yunkurin wata jama’a da ke kiran kanta Malamai, amma ta bari wasu wadanda ba su nufin alheri su yi amfani da su a kawo baraka tsakanin jama’ar Musulmi. Wannan abin takaici ne.

“Tun daga ranar da a ka assasa Majalisa zuwa yau ba a taba samun tabargaza irin wannan ba. Don haka Majalisa ta Kasa na yin kira ga wadannan mutane su tsoraci Allah su kauce ma son zuciya.

“Hakika Majalisar Malamai reshen jihar Kano ta yi daidai da tace wadanda su ka shiga wannan bankaura ba ‘ya’yanta ba ne tun daga jiha balle na Kasa. Yaya za a yi wanda ba ya cikin Majalisa ya ce ya kori wanda a ka kafa Majalisa da shi?.

“A wurin Majalisa ta Kasa abinda a ka yi ba ya bisa doka, kuma wasan yara ne. Hasali ma fata mu ke Allah ya ba shi shugabancinta na Kasa baki daya, amin.

“A karshe, Majalisar kasa ta yi mawafaka da duk abinda Majalisar Kano ta tsaya a Kai. Alhamdu Lillah.”

Continue Reading

Hausa

Tijjanawa ba sa goyon bayan nadin Pakistan shugaban Majalisar Malamai – Alkarmawi

Published

on

Khalifa Abdulmajid Alkarmawi

Khalifa Abdulmajid Alkarmawi

 

 

 

 

بسم الله الرحمن الرحيم 

وصلي الله علي النبي الكريم 

Majalisar Malamai ta jihar Kano tana da mahimmanci ga Musulmin Arewacin Nigeria gaba daya ba Kano ba kawai, don ko ba komai Al’ummar Musulmi suna kara samun hadin kai da magana da murya daya sanadiyar wannan majalisar kuma babban abun bukata shine hadin kan Musulmi.

Amma sabon shugabanci da akai jiya (Litinin) da aka nada Malam Abdallah Saleh Pakistan (Shugaban Izala na jahar kano) zai iya rusa majalisar ma gaba daya, Saboda Shugabancin yana bukatar malamin da yake Zaune lafiya da duk akidun Musulunci da suke Kano, wanda Pakistan kuwa yana da matsala da wasu bangarorin.

Shawarata kowa a nan shine Asami malamin da yaki da kyakkywar alaka da kowa ya jagoranci Alumma Sai asami kai wa ga gaci.

Don haka a madadin Tijjanawa, gaskiya gabadayanmu musamman na jihar Kano muna sanar da cewa ba ma tare da Shugabacin Malam Abdallah Saleh Pakistan.

Khalifa Abdulmajid Alkarmawi

Shugaban Khuddamur Rasul SAW na Afrika

Continue Reading

Hausa

Gamayyar Malaman Kano sun nesanta kan su daga tsige Malam Ibrahim Khalil

Published

on

Sheikh Ibrahim Khalil

Nasiru Yusuf

Gamayyar Malaman Jihar Kano da suka kunshi jagororin darikun Tijjaniyya da Qadiriyya da kuma Salafiyya sun yi watsi da sanarwar tsige Malam Ibrahim Khalil daga shugabancin majalisar malamai.

Wata sanarwa da KANO FOCUS ta ci karo da ita dauke da sa hannun sakataren gamayyar Malaman, Dr Sa’idu Ahmad Dukawa ranar Talata malaman sun ce ba da yawunsu aka dauki wannan mataki ba, kuma ba sa goyon bayansa.

Malaman da suka sahale a fitar da sanarwar sun hada da Shugaban Darikar Kadiriyya na Afrika ta Yamma Sheikh Karibullahi Sheikh Nasiru Kabara da Sheikh Abdulwahab Abdallah da Sheikh Ibrahim Sheh Maihula da Dr. Bashir Aliyu Umar da kuma Imam Nasir Muhammad Adam ( Shugaban majalisar Limaman masallatan Juma’a).

Sauran sun hada da Farfesa Musa Muhammad Borodo da Farfesa Muhammad Babangida da kuma Dr. Ibrahim Mu’azzam Maibushira.

Continue Reading

Trending