Connect with us

Hausa

A gabana Abduljabbar ya ce akwai hadisin fyade a Muslim, amma na duba ban gani ba – shaida

Published

on

Nasiru Yusuf

Shaidar da lauyoyin gwamnatin jihar Kano suka gabatar a gaban kotu yau Alhamis Murtala Kabiru Muhammad ya ce a gabansa Sheikh Abduljabbar ya ce an ruwaito Annabi Muhammad (SAW) ya yi wa Nana Safiyya fyade a Muslim, amma koda ya duba bai ga hadisin ba.

Murtala Kabiru Muhammad ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a cigaba da sauraron karar da gwamnatin jihar Kano ta kai Sheikh Abduljabbar Kabara inda take tuhumarsa da yin 6atanci ga Annabi Muhammad (SAW).

Murtala Kabiru Muhammad ya fadawa Kotu cewa a ranar  Juma’a 10 ga watan Satumba na shekarar 2019 ya halarci karatun da Malam Abduljabbar ke yi a masallacin As’habulkahfi inda Malamin ya ce ya zo cikin Sahih Muslim a hadisi mai lamba 1,360 da 1,428 Annabi ya yi wa Nana Safiyya fyade.

Shaidar ya ce Abduljabbar ya kuma fadawa ma su sauraransa cewa Annabi tirsasawa Nana Safiyya ya yi, ta aure shi. Inda ya ce hakan fyade ne daraja ta farko.

Murtala Kabiru Muhammad ya shaidawa Kotu cewa da kunnensa ya ji Sheikh Abduljabbar ya fadi kalmomin fyade da da auren dole da kwace.

Hakazalika shaidar ya fadawa Kotu cewa a ranar Juma’a 25 ga watan Oktoba, 2019 malam yana Cikin karatu ya ce akwai hadisi a Sahihul Bukhari mai lamba 2,322  inda aka ce “wata mata ta zo wajen Annabi (SAW) tana kwarkwasa, sai ta ce na zo wajenka ne ina sha’awarka. Sai Annabi ya ce mata ta je wani waje ta jira shi. Sai ta tafi. Kuma Annabi ya je ya same ta, ya biya mata bukatarta.”

Mai ba da shaidar ya ce a cikin wani karatu ya ji Abduljabbar ya ce Annabi ya biya mata bukatar ne irin ta namiji da mace.

Ya ce “Don haka wadannan kalmomi da Malam Abduljabbar ya ambata akan Annabi ni Murtala na ji su da kunnena Malam Abduljabbar ya fada na kwarkwasa, sha’awa, biyan bukatar mata da sauransu. Kuma a ranar Juma’a ne.”

Shaida Murtala ya ce, “Da na ji hakan, ban ji dadi ba, don haka na koma na dakko duk wadannan littattafan da ya fada na Bukhari da Muslim na duba duk lambobin da Malam Abduljabbar ya ambata, kuma na duba ni ban ga wadannan kalamai da ya ambata ba.”

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

EFCC arraigns one for N108 million fertiliser fraud in Kano

Published

on

Sanusi Hashim

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

The Kano Zonal Directorate of the Economic and Financial Crimes Commission, EFCC, has arraigned one Sanusi Hashim for allegedly misappropriating and converting to his personal use, the sum of 108 million Naira. 

 

KANO FOCUS reports that Hashim was arraigned before Justice Kabiru Dabo of the Kaduna State High Court sitting in Zaria on a one -count charge of misappropriation contrary to Section 293 and punishable under section 294 of the Penal Code.

 

He was alleged to have collected a total sum of 108 million Naira from one Ahmad Mohammad Liman and Basiru Mohammad for the supply of fertilizer but instead misappropriated and diverted the money for his personal use.

 

The lone-count charge reads ‘’That you Sanusi Hashim sometime in April 2020 under the jurisdiction of the Kaduna State High Court dishonestly misappropriated and converted to your own use, the sum One Hundred and Eight Million Naira (N108,000,000) property of one Ahmad Mohammad Liman and Basiru Mohammad for the supply of fertilizer from Indorama Eleme Fertilizer and Chemicals and you thereby committed an offence under Section 293 and punishable under Section 294 of the Penal Code’’.

 

The defendant pleaded not guilty when the charge was read to him.

 

Counsel to the prosecution, Bright C. Ogbonna prayed the court for a trial date in view of the defendant’s plea.

 

Consequently, Justice Dabo remanded the defendant in a Correctional Centre and adjourned the matter to February 10, 2025 for hearing of bail application.

Continue Reading

Hausa

Gov. Yusuf Directs Reassigned Commissioners to Handover and Assume Duties by Tuesday, 17th December

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

The Governor of Kano State, Alhaji Abba Kabir Yusuf, has directed all reassigned commissioners to ensure a smooth handover and assumption of duties by Tuesday, 17th December 2024.

Speaking through his spokesperson, Mr. Sanusi Bature Dawakin Tofa, the Governor stated that the cabinet changes will take full effect during the next council meeting on Wednesday, 18th December 2024.

He emphasized the need for the completion of all transition processes before then.

“All commissioners affected by the changes are directed to hand over their responsibilities between Monday, 16th and Tuesday, 17th December 2024,” the statement reads.

The Governor further urged members of the state executive council to redouble their efforts and uphold a strong spirit of teamwork, dedication, and commitment to supporting his administration in serving the good people of Kano State.

Continue Reading

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Trending