Connect with us

Hausa

Samarinmu basa zance ranar Alhamis da Juma’a-‘Yan matan Tudun Yola

Published

on

Aminu Abdullahi

‘Yan mata a Tudun Yola na ci gaba da mayar da martani kan dokokin da dagacin yankin ya fitar na takaita zance zuwa ranar Alhamis da Juma’a kawai da yan mata da zawarawan yankin.

Yayin zantawar Kano Focus da wasu yan mata a yankin sun ce ko kadan samarinsu basa zuwa zance ranar Juma’a da Alhamis.

A don haka su ba su amince da wammam doka ba kuma basa maraba da ita tunda dai ba a taba samun wasu da aikata ba dai-daiba.

Idan za a iya tunawa dai a ranar Litinin din da ta gabata ne dagacin garin Tudun Yola Malam Nasidi Hamisu ya fitar da wasu dokoki guda hudu da ya ce ya zama dole al’ummar yankin su bi domin tsaftace garin daga muggan ayyuka.

Dokar ta ce an hana zancen saurayi da budurwa da bazawara ta ci barkatai.

Haka zalika ya ce an samar da lokacin yin zance da bai saba ka’ida ba kamar haka.

Ranar Alhamis da Juma’a kawai, daga karfe 5:00 na yamma zuwa 8:00 na dare.

Daga yanzu Alhamis da Juma’a ne kawai ranar zance a Tudun Yola-Dagaci

Ayi muku kayan daki, ayi muku gara, kuce a soke lefe-martanin ‘yan mata ga samarin Kano

Neman matar aure: Hisba ta kafa kwamitin mutane 5 da zai binciki Uba Rimo

Haka kuma doka ta biyu ta ce an hana kowacce budurwa ko bazawar yin zance a wani wuri da ba Kofar gidan ubanta ba.

Sai kuma doka ta gaba da ta ce an hana yin kidan Dije a yankin Tudu Yola baki daya.

Idan kuma ya zama dole sai an yi to a tuntubi mai garin Tudun Yola domin a bada tsarin yadda za a yi.

Sai doka ta hudu an hana yin shaye-shaye ko kuma sayar da kayan sahye-sahyen a fadin Tudun Yola baki daya.

Sai dai wannan sanarwa ta bar baya da kura, duba da yadda ‘yan mata da samari ke ta yin Allah wadai da ita.

Hafsat Kamal wata budurwa ce da ke yankin ta ce ko kadan bata goyan bayan dokar kasancewa ba a taba kama wasu da suke yin zance da aikata badala ba.

Ta ce da yawan samarin da suke zuwa zance basu da lokacin da za su zo a ranakun Alhamis da Juma’a da aka saka.

“Yawanci ma sai Asabar da Lahadin suke samun lokaci,” a cewar ta.

Khadija Musa ta ce ranakun da aka sanya sunyi kadan, akwai bukatar a kara ranakun zuwa kwana hudu a sati.

“Ni bana goyan bayan hana yin D.J saboda wasu basu da halin da za su kama dakin taro, gaskiya bama goyan baya,” inji Khadija.

Umar Yusuf da ya shafe shekaru biyar a unguwar ya ce, dokar takaita zance da haramta D.J abune mai kyau, duba da yadda yinsa ke tada zaune tsaye.

Ya ce a wasu lokutan ana samun rigima dazarar anyi kidan D.J.

Bamusan da dokar ba

Sai dai a nasu bangaren masu sanar D.J a unguwar sunce basu san da dokar ba, don kuwa babu wanda ya zauna da su kafin zartas da ita.

Shugaban kungiyar masu sana’ar D.j na unguwar, Yusuf Umar ne ya bayyana hakan, inda ya ce ba a gayyace su ba kafin zartas da dokar.

Ya kara da cewa zargin da ake musu ba gaskiya bane kuma za su cigaba da gudanar da sana’arsu a unguwar kamar yadda suka saba.

“Babu wanda ya sanar da mu ko aiko mana da kwafin dokar muma gani mukayi a yanar gizo.

Ya ce don haka zamu cigaba da yin sana’ar mu tunda muna da rijista da hukumar tace fina-finai ta jiha,” a cewar sa.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Mahaya dawaki sun kashe mutune 2 a Kano

Published

on

Aminu Abdullahi

Wasu magidanta biyu ‘yan gida daya sun rasu sakamakon banke su da mahaya Dawaki su ka yi yayin da suka bisa babur a titin  Sokoto Road da ke Kano.

Kano Focus ta ruwaito cewa ranar Asabar ne mahaya Dawakin suka kashe Inuwa Sani da Abdulrahaman Sani ‘yan unguwar Yakasai a Birnin Kano.

Mahaifiyar su, Rukayya Ali ta ce an kashe ‘ya’yan na ta ne akan hanyar su ta zuwa gaishe ta.

Ta ce kowanne daga cikin marigayan  ya mutu ya bar mata daya  daya ‘yaya shida.

Rundunar ‘yan sandan Kano ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin kakakinta Abdullahi Haruna Kiyawa.

Ya ce suna zargin wani matashi Sadiq Adamu, 22, da abokansa bakwai ne suka shirya hawan Dawakin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutanen.

Ya ce sun kama biyu daga cikin wadanda ake zargi kuma da zarar an kammala bincike za a gurfanar da su gaban kotu.

Masarautar Kano dai ta haramta hawan Dawaki a cikin birinin Kano sakamakon jikkatawa ko hallaka jama’a da mahayan ke yi.

Continue Reading

Hausa

Kishi: Mata a Kano ta hana a yiwa mijinta jana’iza a gidansa

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

Tsananin kishi ya sanya wata mata Jamila Muhammad hana shigar da gawar mijinta cikin gidansa domin yimasa jana’iza bayan rasuwarsa.

KANO FOCUS ta ruwaito al’amarin ya faru ne ranar Litinin a unguwar Gwazaye da ke yankin Dorayi a karamar hukumar Gwale, da ke nan Kano.

Abdullahi Mustapha guda ne daga cikin wadanda suka sheda al’amarin ya shaidawa shirin ‘yan zazu na gidan rediyon Dala cewar tsananin kishi ne ya hana matar amincewa a ajiye shi a gidanta.

Ya ce matar na zaune ne a gidan mijin bayan da kotu ta raba aurensu ta kuma umarceshi da ya bata dama ta ci gaba da zama a gidan saboda yara.

Ya kara da cewa matar ta nemi su rabu da mijin ne don kawai ya auri wata matar.

Sai dai bayan auren sabuwar matar ne kuma auren ya rabu, haka kuma gidan ya koma hannunta.

Mustapha ya ce bacin rai da takaicin matar ne ya haifarwa mijin ciwon zuciya har ya mutu.

Bayan mutuwar tasa ne kuma aka daukoshi daga asibiti aka kuma kaishi gidan da matar take amma fafur ta ce ba za a yi masa sutura a gidan ba.

A cewar Mustapha ba irin bakin da ba a baiwa Jamila ba, amma ta ce sai dai a kaishin gun amarya a yi masa jana’iza.

Hakan ta sanya wani dattijo a unguwar ya bada damar a shigar dashi gidansa domin yi masa jana’iza.

Tuni dai yan uwan Jamila suka dauke ta zuwa garinsu da ke Gezawa domin gudun abinda zai faru.

Continue Reading

Hausa

Hisbah ta nemi taimakon Saudiyya kan dakarunta

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta nemi taimakon kasar Sadiyya da ta tallafa mata wajen horar da jami’anta akan sha’anin aikinsu.

Kano Focus ta ruwaito babban Kwamandan Hisbah, Muhammad Harun Sani Ibn Sina ne ya yi rokon a ofishinsa ranar Lahadi.

Wanan na zuwa ne bayan da hukumar ta karbi bakuncin daya daga cikin limaman Masallacin Harami na Makkah Farfesa Alhassan Bin Abdulhameed Albukhary tare da ayarinsa.

Ayarin Limanin sun ziyarci Kano ne bisa gayyatar Jami’ar Bayero don horarwa ta musamman ga alkalai da daliban ilimi wanda wannan ita ce horarwa irinta ta hudu da suka yi a kasar nan.

Hisbah ta kama matar da ta yi safarar jariri daga Delta zuwa Kano

Ramadan:Hisbah ta kama Gandaye 11 a Kano

Shigar mata: Hisba ta kama wani saurayi da ya rikide zuwa Amina a Kano

“Babban kalubalenmu shi ne rashin wurin da za mu horar da jami’anmu domin su kara samun horo a kan ayyukansu.

“Zai yi kyau idan har za mu samu tallafi daga Hukumar Kasar Saudiyya mai albarka wajen samar mana da wuri ko kuma makarantun da jami’anmu za su dinga samun horo ko da kuwa a kasar Saudiyya din ne.” cewar Ibn Sina

A nasa Jawabin Imam Albukhariy ya yaba wa hukumar Hisbah akan ayyukan da take gudanarwa a fadin jihar nan, inda ya nemi su rubanya kokarinsu akan ayyukansu.

“Shi aikin umarni da aikin alheri da hani da mummuna abu ne babba a harkar zamantakewar al’umma.

“Wasu malamai suna cewa da za a kara wani abu a kan rukunan Musulunci to da abin da za a kara ba zai wuce umarni da aikin alheri da hani da mummuna ba saboda muhimmancinsa a Musulunci.

“Don haka ’yan Hisbah ku sani aikin Allah kuke yi.”

Farfesa Albukhari wanda shi ne Shugaban Sashen Larabci na Jami’ar UmmulQura da ke garin Makkah ya bayyana cewa, Hukumar Kasar Saudiyya za ta taimakawa hukumar Hisbah da duk irin abin da take bukata, matukar dai bai ci karo da tsarin mulkin kasar ta Saudiyya ba.

Continue Reading

Trending