KANUN LABARAI
Jam’iyyar APC a Kano na yunkurin hallakani-Saha’aban Sharada
Aminu Abdullahi
Dan Majalissar tarayya mai wakiltar karamar hukumar birni Sha’aban Ibrahim Sharada ya zargi jam’iyyar APC ta jihar Kano da bada umarnin hallakashi.
Sha’aban Sharada ya ce jam’iyyar ta bada umarnin ne yayin zaben fidda gwani na ‘yan takarar shugabancin kujerar shugabancin karamar Hukumar ta birni.
Kano Focus ta rawaito dan majalisar ya bayyana hakanne ya yin hirarsa da Freedom Radiyo ranar Lahadi.
Ya ce shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar birni Malam Sani Fata da makarrabansa sun yi amfani da sojojin haya amatsayin shugabanin mazabu, da su ne su kayi dangwale ba ainihin shugabanin jam’iyyar na mazabu ba.
Ya kuma ce akwai wasu manya da ke tare da gwamnati su biyu a karamar da suka turo da yan daba domin tarwatsa taron, kuma su hallakashi.
A cewarsa hakan ta sanya ba shiri shi da magoya bayansa suka bar wurin da ake gudanar da zaben
Da gangan aka raba kan jam’iyya
Sha’aban Sharada ya ce da gangan aka bar jam’iyyar APC ta rabu gida biyu a karamar hukumar Birnin zuwa bangaren dake samun goyan bayan gwamnati da kuma bangaren sa dake samun temako daga Allah.
“Kamar yadda yake idan aka gaza samun sulhu tsakanin ‘yan takara ana gudanar da zaben fidda gwani to a karamar hukumar birni ma haka ce ta kasance.
“Bangaren gwamnati sun bada nasu dan takarar Hafizu Alfindiki muma bangaren mu mun tsaida Murtala Sunusi Dandawaki,” a cewar sa.
Malam Sharada ya sun biya kudin form na takarar shugabancin karamar hukumar dana kansiloli goma sha uku naira miliyan daya da dubu dari takwas.
Amma jam’iyyar taki basu fom din har saida suka rubuta takadar korafi zuwa ga shugabancin jam’iyyar na jiha kana daga baya ana sauran kwana daya a gudanar da zabe aka basu fom din.
“A ka’ida idan muka cike zamu kaiwa jam’iyya matakin karamar hukuma su sa hannu,daga nan mukai matakin jihar amma bisa mamaki bayan mun cike fom din saida muka yini muna neman wanda zai karba yasa hannu amma mun rasa.
“Jam’iyyar APC tayi taro ne kawai tare da sanar da son zuciyar su maimakon bari a fafata a zaben fidda gwani,” inji Sharada.
Siriki ne ya ya jagoranci zaben
Sha’aban Sharada ya ce jam’iyya ta turo mutum biyu a matsayin turawan zabe da daya daga cikin su sirikin Baffa Babba ne.
Ya kara da cewa shugabannin jam’iyya a karamar Hukumar birni da kudin tsarin jam’iyyar ya nemi su yi zabe su dari uku da tamanin ne.
Amma dari hudu da hudu ne suka kada kuri’a, da hakan ke nuna sun wuce adadin da kundin tsarin mulki ya tanada.
“wai mutum dari hudu sun zabe su mu kuma dan takarar mu ya samu kuri’a hudu.
“Lokacin da muka je filin zabe sai aka hana ainihin shugabanin jam’iyya katin makalawa da zai basu damar shiga suyi zabe,” inji shi.
Ya kara da cewa da anyi zabe kamar yadda kundun tsarin mulkin jam’iyya ya tanadar tabbas za su karbi kowanne irin sakamako.
“Kiri-kiri baturen zabe Yusuf Lajawa ya ce ba zaibi kundun tsarin mulkin jam’iyya ba, shi zayyi amfani da umarnin Abdullahi Abbas ne kawai.
Malam Sharada ya kuma ce suna shirye-shiryen daukar matakin da ya dace akan irin kama karyar da akayi masu.
Hausa
Mutane 18,000 sun amfana da aikin ido kyauta ta Gidauniyar Mangal a Katsina
Kimanin marasa lafiya masu rauni 18,000 da ke fama da cututtukan ido daban-daban a jihar Katsina sun amfana da ayyukan kulawar ido da tiyata kyauta da Gidauniyar Mangal ta dauki nauyi tun bayan kafuwarta a shekarar 2016.
Wani mamba na kwamitin amintattu (Board of Trustees) na gidauniyar, Malam Hussaini Kabir, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a yayin kaddamar da aikin tiyatar ido na zangon karshe na shekarar 2025 a Cibiyar Ido ta Katsina.
Kabir ya bayyana cewa kimanin mutane 7,000 ne suka amfana a shekarar 2025 kadai, daga sassan jihar Katsina, jihohin makwabta, har ma da wasu yankuna na Jamhuriyar Nijar.

A cewarsa, gidauniyar ta fara tantance wadanda za su amfana kimanin makonni biyu da suka gabata, inda marasa lafiya da dama suka samu magunguna kyauta da tabarau na likita.
Kabir ya kara da cewa wadanda ke bukatar tiyata an dauki nauyin dukkan zaman asibitinsu gaba daya, yana mai cewa kimanin marasa lafiya 2,000 aka tantance a yayin aikin zangon karshe da ake ci gaba da yi.

Ya sake jaddada kudirin gidauniyar na inganta samun kulawar lafiya, yana bayyana shirin a matsayin wani bangare na nauyin alhakin zamantakewar kamfanoni (corporate social responsibility).
“Manufarmu ita ce tallafa wa kokarin gwamnati tare da rage nauyin kudin kula da lafiya ga mafi rauni, musamman wadanda ke fama da matsalar biyan bukatun rayuwa,” in ji shi.

Wani likitan ido a cibiyar, Dokta Ahmad Hamza, ya bayyana cewa an gano marasa lafiya da dama na fama da cutar idon toka (cataract) da glaucoma, cututtuka da galibi ke bukatar tiyata.
Ya jaddada muhimmancin duba ido akai-akai, yana mai cewa gano cuta da wuri na taimakawa wajen hana asarar gani ta dindindin da cututtukan ido masu zuwa a boye ke haifarwa, kamar glaucoma, cataract da lalacewar macula (macular degeneration).

Daya daga cikin wadanda suka amfana, Malam Yusufa Usman, ya ce ya shafe sama da shekaru biyu yana fama da matsalar gani amma ba shi da ikon biyan kudin tiyata.
“Tsawon shekaru biyu ban iya gani sosai ba, amma yau na yi tiyata kuma ina da fatan ganina zai dawo.
Ina rokon Allah Madaukakin Sarki ya saka wa Gidauniyar Mangal da alheri bisa wannan kyakkyawan aiki.
“Ina fatan sauran masu kudi za su yi koyi da wannan abin a yaba,” in ji Usman.

Wata mai amfana, Aisha Muntari daga kauyen Bakuru, ta bayyana kwarewarta yayin da take jiran a kai ta dakin tiyata.
Muntari ta ce ta kamu da matsalar ido kimanin shekara guda da ta wuce kuma ta kusa yanke tsammani kafin ta samu labarin shigar gidauniyar, tana mai bayyana kwarin gwiwar cewa nan ba da dadewa ba ganinta zai dawo.
Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano
Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”
Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye
Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.
Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.
